Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

  • Ministan shari’a, Abubakar Malami ya bada kwangilar karbo kadarorin da aka sace ga wani kamfani
  • Babban lauyan gwamnatin tarayya ya zabi Gerry Ikputu & Partners su yi wannan aiki da za su ci biliyoyi
  • Kamfanin zai yi kokarin karbo kadarorin gwamnati da aka rasa, sannan za a ba su 3% a abin da aka samu

A wani rahoto na musamman da Premium Times ta fitar, an ji cewa Abubakar Malami ya ba Gerry Ikputu & Partners kwangilar karbo kadarorin gwamnatin tarayya.

Wannan kamfani ya dauki hayar lauyoyin M. E. Sheriff & Co su taya shi wannan aiki na bi jihohi 10 da Abuja domin a karbo filaye da dukiyar gwamnatin Najeriya.

Za a ba kamfanonin nan 3% na duk abin da suka yi nasarar dawo da shi ga hannun gwamnati. Ministan shari'a ya haramtawa kamfanonin fadin sirrin aikin na su.

Kara karanta wannan

Karshen Korona: Jirgi zai fara jigila daga Dubai zuwa Najeriya ranar 5 ga wata

Jaridar ta ce akwai yarjejeniya da aka yi kafin a bada kwangilar cewa kamfanonin ba za su taba fadawa Duniya aikin da suke yi ba sai sun samu izinin hakan daga AGF.

Sashen ARMU na ma’aikatar shari’a ta ce wannan sharadi bai nufin ana nuku-nuku wajen aikin, sai dai kurum ka’ida ce da aka saba amfani da ita wajen wannan aiki.

Malami ya ba kamfanin na M.E Sherriff &Co watanni shida ne domin ya kammala aikin. Ana sa ran cewa za a kammala komai daga Oktoba 2021 zuwa Afrilun 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Buhari
Ministan shari'a, AGF Abubakar Malami SAN Hoto: Facebook / Abubakar Malami
Asali: Facebook

Kadarorin da za a karbe

Cikin kadarorin da ake so kamfanonin su dawo da su hannun gwamnati akwai gine-gine 74 a Legas, Ribas, Akwa Ibom, Abia, Anambra, Edo, Enugu, da jihar Imo.

Sahara Reporters ta ce akwai wasu dukiyoyin a Kuros Riba, Delta da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Jihohi za su sake sa kafar wando daya da ‘Yan Majalisa kan rigimar dokar zabe

A jihar Abia akwai gidan tarihin yaki, Ojukwu Bunker a Umuahia, da cibiyar National Research Institute, a garin Umudike. A Fatakwal akwai filaye da gidaje takwas.

A jihar Legas kuwa akwai filaye a Alexander Avenue a Ikoyi, Lekki Phase 1 da wasu kango a Victoria Gardens City da kuma wani gida a titin Wharf Road a Apapa.

A Abuja ana son karbe GSM Village da ke Wuse Zone 1 da wasu filaye a unguwar Mabushi. Haka zalika akwai gine-gine da wasu gidajen da ake hari a jihar Anambra.

Ministan shari’a zai bada 3%

A duk kadarorin da aka yi nasarar karbowa, Gerry Ikputu and Partners su na da 3%. Za a biya su kason na su ne bayan dukiyoyin sun shiga hannun gwamnatin tarayya.

Yarjejeniyar ta ce bankin CBN zai biya wannan kudi idan an yi lissafi. Tuni dai lauyoyi suka fara sukar wannan kwangila, gwamnati kuwa ta ce babu dokar da aka saba.

Kara karanta wannan

Gwamnan bankin CBN ya bude katafaren kamfanin shinkafa da zai taimakawa Jihohin Arewa

Masana su na ganin facaka za ayi da dukiyar da wasu suka dauke, ARMU ta ce ba haka abin yake ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel