Babbar Magana: Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus

Babbar Magana: Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus

  • Yayin da APC ta ƙasa ke shirin gudanar da babban taronta a wannan watan, a jihar Gombe sabon rikici ne ya sake kunno kai
  • Hadimar gwamnan jihar, Dijjatu Bappa, da wasu manyan jiga-jigan APC reshen Gombe sun yi murabus daga APC baki ɗaya
  • Tsohon kwamishinan lafiya da kuma tsohon ɗan takarar gwamna na daga cikin waɗan da suka fice daga APC a Gombe

Gombe - Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ya ɗauki wani sabon salo ranar Laraba da daddare yayin da manyan jiga-jigan jam'iyya suka yi murabus.

The Nation ta rahoto cewa waɗan da suka yi murabus daga APC ɗin sun haɗa da, tsohon kwamishinan lafiya, Dakta Ahmed Gana, mai baiwa gwamna shawara, Dijjatu Bappa, da babban jigo Jamil Isyaka Gwamna.

Murabus da ficewa daga APC na Bappa da kuma Gwamna ya biyo bayan sauya shekar Dakta Ahmed Gana zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya kwana biyu da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Allah ya mun wahayi, Gwamnan PDP ya faɗi sunan wanda zai gaji kujerarsa a 2023

Tambarin APC
Babbar Magana: Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Bappa, a wata takarda da ta aike wa gwamnan mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Fabrairu, tace ta yi murabus nan take.

Hadimar gwamnan ba ta bayyana dalilin murabus ɗin ta ba, amma dai ta shaida wa gwamnan jihar cewa ta aje aikin ta na mai bada shawara kan zuba hannun jari.

Kazalika, fitaccen ɗan kasuwan Gombe kuma babban jigon APC, Dakta Jamil Gwamna ya yi murabus daga kasancewarsa ɗan jam'iyyar APC.

Gwamna, ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar Gombe ƙarƙashin inuwar jam'iyyar hamayya PDP a zaben 2019 da ya gabata, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Sai dai ya koma APC a 2019 tare da dubbannin magoya bayansa, inda suka taka rawar gani wajen nasarar zaɓen gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Yari da Marafa sun gana da Atiku da Saraki

Meyasa ya fice daga APC?

A takardar murabus ɗinsa wacce ya aike wa shugaban APC na gundumar Jekadafari, yace ya yanke hukuncin ficewa ne bayan dogon nazari da shawari da iyalansa, abokan siyasa da masoya.

Wani sashin wasikar yace:

"Tare da dukkan girmama wa ina mai sanar maka na yanke hukuncin murabus daga APC mai mulki. Na ɗauki wannan matakin ne bayan shawari da iyalaina, abokanan siyasa da masoya."
"Na gode da duk wata alfarma da akayi mun a jam'iyya lokacin ina cikinta, kuma ina wa APC fatan Alkairi."

A wani labarin na daban kuma Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zai ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubabar, yace ba da jimawa ba zai fito ya bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Atiku ya kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, bisa karuwar hare-haren yan bindiga a jiharsa, daga bisani ya garzaya gidan tsohon shugaban ƙasa IBB.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Zan sasanta da Ganduje amma bisa Sharaɗi ɗaya, Shekarau ya magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel