Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

  • Mambobin jam'iyyar APC reshen Ingila, sun ziyarci Jagaban, Ahmed Bola Tinubu, bayan kwana 2 da saukarsa kasar
  • Tsohon gwamnan Legas din ya tafi halartar taruka da ganawa da jama'a ne kamar yadda Tunde Rahaman ya bayyana
  • Wannan tafiyar na zuwa ne bayan makonni da jigon jam'iyya mai mulkin ya bayyana burinsa na shugabantar Najeriya

'Ya'yan jam'iyyar APC da ke zaune a Ingila sun kai wa Bola Tunubu, shugaban kuma jigon jam'iyyar ziyara a gidansa da ke can.

Ziyarar ta zo ne bayan kwana biyu da saukar Tinubu a birnin Ingila.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya je UK ne domin "halartar taruka da ganawa da jama'a", kamar yadda Tunde Rahman, mai magana da yawun sa na kafafan sada zumuntar zamani ya bayyana.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

A farkon watan nan, Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya tabbatar masa kudirin sa na neman kujerar shugabancin kasa a shekarar 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya siffanta zama shugaban kasar Najeriya a matsayin "burin da ya dade ya na mafarki"

Ga hotunan su.

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

A wani labari na daban, wani lokacin, ‘yan siyasa su na shirya komai kafin su sauka daga wani mukami wanda daga bisani sai su yi kamar dama faruwa ya yi ba tare da shirinsu ba.

A ranar Litinin, Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam’iyyar APC, ya sanar da manema labarai cewa ya fada wa shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

Sai dai hakan bai ba jama’a mamaki ba saboda yadda Tinubu ya dade yana kamfen din shugabancin kasa tun kafin ya yi maganar a Aso Rock.

Sai dai tambayar da ‘yan Najeriya da dama su ka dinga yi shi ne, “meyasa sai yanzu?”

A watanni 2 da suka gabata, Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, wanda ya gaji mulkin jihar Legas a 2007, ya bayar da wannan tsokacin.

Yayin wata tattauna da Channels TV ta yi da shi a wani shiri na ‘Hard Copy’, an tambayi Fashola idan yana goyon bayan takarar Tinubu, inda ya amsa da cewa:

“Mun hadu a makon da ta gabata; amma bai sanar da ni cewa zai tsaya takara ba kuma cewa ya yi a wata takarda da ya saki cewa zuwa watan Janairu kowa zai san abinda ake ciki,” a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel