'Yan daba sun banka wa sakatariyar PDP da ofishin kamfen din Atiku wuta a Gombe

'Yan daba sun banka wa sakatariyar PDP da ofishin kamfen din Atiku wuta a Gombe

  • Wasu 'yan daba sun kai hari sakatariyar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da ke Jihar Gombe, sun yi barna sun cinna wuta
  • Wani mai goyon bayan jam'iyyar PDP a Gombe, Muntari Kulsi, ya yi ikirarin cewa yan daban yan jam'iyyar APC ne suka kai harin
  • Kulsi ya bayyana yadda yan daban suka zo cikin motocci dauke da makamai suka fattaki masu gadi kafin suka tafka ta'adin

Jihar Gombe - Wasu yan daban siyasa, a safiyar ranar Talata, sun banka wa sakatariyar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, wuta a Jihar Gombe, rahoton TVC News.

Ita ma The Punch ta rahoto cewa an cinna wa ofishin da ke kan babban titin Gombe/Bauchi da na Atiku House wuta, hakan yasa aka yi asarar kayayyaki, kujeru da wasu abubuwa masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Da Ɗuminsa: 'Yan daba sun banka wa sakatariyar PDP wuta a Gombe
Yan daba sun kai hari sakariyar PDP a Gombe, sun kona ofishin shugaban jam'iyya. Hoto: The Punch
Source: Twitter

Wani dan PDP ya yi ikirarin yan APC ne suka cinna wutan

Wani magoyin bayan jam'iyyar, Muntari Kulsi, ya yi bayanin cewa an cinna wa ofishin wuta ne mislain karfe 1.30 na dare, yana mai cewa ya baro sakatariya misalin karfe 1.20 na dare.

Ya ce wadanda ake zargin yan daban ne yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ne yana mai cewa ba zai yiwu dukkan ofisoshin biyu su yi gobara ba a lokaci guda tunda ba kusa suke ba.

Kulsi ya ce:

"Jam'iyyar APC da mutanen ta ne suka aikata. Akwai tazarar kilomia hudu tsakanin ofisohin don haka ba zai yiwu su kama wuta lokaci daya ba.
"Mutanen mu da ke nan sun ga yan daban, sun taho a motocci uku da makamai masu yawa, yan daban sun fi karfin masu gadin wurin don haka suka tsere don tsira da ransu."

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Rimin-Gado, ya koma PDP

A cewarsa, jami'an hukumar kwana-kwana da ke kusa da ofishin sun yi kokarin kashe wutan, shima DPO na yan sanda a Pantami shima ya taimaka.

"Muna jira ne shugabannin mu su zartar da matakin da za a dauka, amma mun san wadanda suka aikata wannan abin kuma za mu dauki mataki kansu," in ji shi.

An yi kokarin ji ta bakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Muritala Usman, yayin hada wannan rahoton amma ba a same shi ba.

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

A wani labarin, Jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi a ranar Juma’a ya kalubalanci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Showunmi wanda tsohon kakakin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ne, Tambuwal da Saraki ba sa da gogewar da za su iya mulkar cukurkudaddiyar kasa kamar Najeriya.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Ya tsaya akan cewa Atiku ne kadai wanda ya fi dacewa ya tsaya takarar a PDP kuma ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164