Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

  • Asiwaju Bola Tinubu ya ba da kyautar kudade ga gwamnatin jihar Neja domin magance matsalar tsaro a jihar
  • Ya yi wannan kyautar ne bayan da ya kai ziyara jihar a yau Alhamis 20 ga watan Janairun wannan shekarar
  • Ya kuma gana da Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya kan batun da ya shafi tsayawarsa takara

Minna, Neja - Jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma mai neman takarar shugaban kasa a 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya baiwa gwamnatin jihar Neja gudunmawar Naira miliyan 50 domin ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Tinubu ya bayar da tallafin ne a wata ziyarar da ya kai gidan gwamnati da ke Minna inda Gwamna Abubakar Sani Bello ya karbe shi a ranar Alhamis.

Tinubu ya yi kyautar kudi ga 'yan Neja
Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga gwamnatin Neja | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Depositphotos

Kungiyar goyon bayan Tinubu ne ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook jim kadan bayan ziyarar, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

Kungiyar ta rubuta cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Asiwaju a Minna, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar domin magance kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.”

Tallafin na zuwa ne kwanaki bayan da jigon na jam’iyyar APC ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga iyalan wadanda aka kashe a baya-bayan nan a kananan hukumomi biyu na jihar Zamfara.

Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

Kafin ba da kyautar kudin, Bola Tinubu ya kai ziyara Minna, babban birnin jihar Neja domin ganawa da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (rtd).

Tinubu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya isa gidan Janar Babangida da misalin karfe 2:30 na rana, inda su biyun suka shiga wani taro kai tsaye bayan zuwansa.

Ziyarar da Tinubu ya kai wa Janar Babangida (rtd) wanda aka fi sani da IBB ya yi ta ne bayan ganawa da wasu jiga-jigan shugabanni a Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

A wani labarin, tsohon Gwamnan jihar Legas, kuma jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bada gudunmuwan N50million ga iyalan wadanda aka kashe kwanakin nan a jihar Zamfara.

Tinubu ya bada wannan gudunmuwar ranar Alhamis yayinda ya kai ziyara jihar, rahoton Channels.

Asiwaju ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel