Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

  • Bayan an yi ta dogon lissafi, an yi watsi da maganar shigo da Goodluck Jonathan cikin Jam’iyyar APC
  • A baya ana ta rade-radin cewa wasu kusoshin APC daga Arewa su na zawarcin tsohon Shugaba Jonathan
  • An yi la’akari da wasu dalilai, an ga da kamar wuya tsohon shugaban kasan ya iya kai labari a zaben na 2023

Abuja - Rahotanni sun bayyana a game da yadda yunkurin shigo da Dr. Goodluck Jonathan, da ba shi takara cikin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa ya ruguje.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a makon da ya wuce inda ta bayyana cewa kokarin da wasu ke yi na zawarcin Jonathan zai iya kawowa Rotimi Amaechi cikas.

Rahoton na Saturday Vanguard ya nuna cewa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN da wasu na kusa da shi ne suka yi ta zawarcin shugaba Jonathan.

Kara karanta wannan

Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

Daga cikin masu wannan shirin akwai gwamnonin APC biyu daga Arewa maso yamma da kuma gwamna guda da ya fito daga bangaren Arewa maso gabas.

Jagororin na APC sun kuma dauko hayar wani mutumin jihar Kebbi wanda ya rike mukami a gwamnatin Jonathan, domin su cin ma wannan manufa a 2023.

Jonathan da Buhari
Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari Hoto: Facebook / Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Duk da cewa wadannan mutane su na da karfi a gwamnatin Muhammadu Buhari, maganar ta lalace a Aso Villa. Jaridar Reuben Abati ta tabbatar da wannan.

Mutane za su zabe shi kuwa?

Daga cikin abin da ya sa aka ki karbar wannan shawara shi ne ganin wahalar mutane su sake zaben wanda suka fatattaka shekaru takwas da suka wuce.

Wata majiya ta ce an yi tunanin ta ina za a kalli 'yan Najeriya a fada masu Jonathan ne mafita a 2023.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Rotimi Amaechi

An kuma yi la’akari da sha’anin Ministan sufuri na tarayya, Rotimi Amaechi. Wasu manya a fadar shugaban kasa su na duba rawar da Amaechi ya taka a 2015.

A lokacin yana gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi su na cikin kashin bayan da suka karya PDP, musamman a yankin da shugaba Goodluck Jonathan ya fito.

Baya ga wahalar karbuwar Jonathan ga al’umma, shigo da shi APC zai iya zama cin fuska. Akwai wadanda har yanzu ba su yafe abin da Jonathan ya yi masu ba.

Siyasar APC

A makon nan ne mu ka ji ‘Dan autan cikin masu neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Saliu Mustapha ya samu gagarumar goyon baya daga yankin Arewa.

Jiga-jigan jam’iyyar APC daga jihohin Arewa maso tsakiyar Najeriya suna tare da Mustapha yayin da Bola Tinubu yake goyon bayan Sani Musa ya zama shugaban APC.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel