Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023

Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023

  • An gargadi jam'iyyar adawa ta PDP da kada ta mika tikitin takarar shugaban kasa ga duk wanda ya haye shekaru 70
  • Wata kungiyar matsin lamba a cikin jam'iyyar wato Action 2023, ta yi wa PDP wannan gargadi ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Janairu
  • A cewar kungiyar ta matsi, akwai ’yan jam’iyyar matasa da dama wadanda cancantarsu ta dace da aikin shugabancin Najeriya

FCT, Abuja - Wata kungiyar matsi da ke da alaka da jam’iyyar PDP ta yi gargadi kan bayar da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ga duk wanda ya dara shekaru 70 da haihuwa.

Yayin da ta fitar da shawarar kayyade shekarun duk wanda zai karbi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Action 2023, ta ce samun dattijo a matsayin dan takarar jam’iyyar zai karya nasasar jam’iyyar ta samu nasara a zaben.

Kara karanta wannan

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

Jam'iyyar PDP ta ce bata yarda tsoho ya tsaya takara ba
Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023 | Hoto: vanguardngr.com

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Rufus Omeire, Action 2023 ta ce ya kamata jam’iyyar PDP ta kara kaimi ta hanyar haskaka masu neman takarar da suke tsakanin shekaru 50.

Vanguard ta rahoto cewa Omeire ya yi nuni da cewa, akwai matasa masu neman tsayawa takara da yawa a cikin jam’iyyar kuma ya kamata PDP ta yi amfani da su a wannan karon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Raddi ga wasikar tsohon kakakin Atiku Abubakar

Martanin kungiyar kan batun dan takara ya biyo bayan kalaman da tsohon mai magana da yawun Atiku Abubakar, Segun Sowunmi ya yi kan uban gidansa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Sowunmi ya aike da wata wasika zuwa ga gwamnonin jam’iyyar PDP inda ya bukaci a yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin shugabancin yara da rikon yara na PDP.

Kara karanta wannan

'Dalar shinkafar karya': PDP ta yi martani kan bikin bude dalar shinkafar gida ta Buhari

Sai dai a martanin da ya mayar, Omeire ya ce dangane da gogewar da ta dace wajen yin babban aikin takara a 2023, Atiku ba shi da abin da ake bukata na gwamnati ko kuma gogewar tafiyar da kamfanoni masu zaman kansu.

Omeire ya ce:

"Da yake magana a kan gogewar da ya yi a kan aikin, watakila Sowunmi ya yi magana game da halin ubangidansa ne na barin jirgin ruwa a tsakiyar teku, yadda ya yi wa PDP bayan zaben shugaban kasa na 2019."

A wani labarin, tsohon Kwamishinan Ilimi a Jihar Akwa Ibom, Mr Moses Essien, ya ya ce 'yan Najeriya suna son tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya dawo ya jagoranci kasar, The Punch ruwaito.

Essien, wanda shine shugaban kungiyar yakin neman zaben Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce:

"Masu iya magana na cewa, haja mai kyau yana siyar da kansa, domin yana da kyau, da kansa zai rika sayar da kansa. Wannan shine abin da muka gani game da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: 'Yan kamfen din Atiku sun yi watsi dashi sun kama wani dan takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel