Zamfara: Matawalle ya sake nada sabbin hadimai 250, jimillar masu rike da mukaman siyasa 1,700

Zamfara: Matawalle ya sake nada sabbin hadimai 250, jimillar masu rike da mukaman siyasa 1,700

  • Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya sake nada masu mukaman siyasa 250 a jiharsa domin inganta ayyuka da janyo mutanen karkara kusa da gwamnati
  • Alhaji Mikailu Aliyu, Direkta Janar na Harkokin Siyasa da Alaka Tsakanin Jam'iyyu, ne ya sanarwa manema labarai hakan a Gusau
  • Ya ce tun bayan kafa gwamnatin, gwamnan ya nada kwamishinoni 25, mashawarta na musamman 55, Manyan direktoci 72 da mambobin kwamitin amintattu 12

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya kara nada sabbin masu rike da mukaman siyasa a jihar don taimakawa wurin gudanar da ayyukan gwamnati, The Nation ta ruwaito.

Direkta Janar na Harkokin Siyasa da Alaka Tsakanin Jam'iyyu, Alhaji Mikailu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Gusau, ranar Laraba.

Zamfara: Matawalle ya sake nada sabbin hadimai 250, jimillar masu rike da mukaman siyasa 1,700
Gwamnan Zamfara ya sake nada sabbin hadimai 250. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara

Aliyu ya ce dalilin nada sabbin hadiman shine don tabbatar da ganin romon demokradiyya ta kai ga mutane a kauyuka da karkara.

Ya ce tun bayan kafa gwamnatin, gwamnan ya nada kwamishinoni 25, mashawarta na musamman 55, Manyan direktoci 72 da mambobin kwamitin amintattu 12.

Ya ce wadanda aka yi wa nadin mukaman siyasan 250 sun hada da manyan direktoci guda takwas, manyan mashawarta na musamman 242 hakan ya kawo jimillar masu mukaman siyasa a jihar zuwa 1,700.

Gwamnatin Matawalle bata musgunawa kowa, Aliyu

Mikailu Aliyu ya kuma yi watsi da zargin da ake yi na cewa gwamnatin jihar tana bibiyan wani Shamsu Shehu, Shugaban Marafa Social Media, yana mai cewa zargin bata da tushe.

Ya ce gwamnatin Matawalle mai son zaman lafiya ne kuma tana bawa kowa 'yancin tofa albarkacin bakinsa da shiga duk jam'iyyar da ya ke so a jihar.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel