2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

  • Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wadanda suke son aikata rashawa ne ba su son a sake samun wani Buhari a 2023
  • Cikin sanarwar da Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, ya lissafa nasarorin da Buhari ya samu a yayin da gwamnatinsa ke mulki
  • Shehu ya ce wasu manyan yan siyasa ne da ba su ji dadin yadda Buhari ya dakile sata ya kuma ke yi wa talakawa aiki ba, suka kosa ya sauka

Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

2023: 'Manyan mutane' masu sace dukiyar mutane ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
Garba Shehu ya ce manyan 'yan siyasa masu son rashawa ne ba su son a sake samun wani Buhari a 2023. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Wadanda suke son su cigaba da sace dukiyar talakawa ne suka kosa Buhari ya sauka

A cewarsa, wasu manyan yan siyasa a kasar sun kosa wa'adin Buhari na biyu ya kare domin suna fatan su koma 'yadda suke yi a baya su cigaba da wadaka da kudin al'umma' ba kakkautawa, rahoton Daily Trust.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Manyan yan siyasa da yawan a kasar nan sun kosa wa'adin Buhari na biyu ya kare. Suna son komawa gidan jiya inda suke sace kudaden al'umma suna karkatar da su zuwa kasashen waje cikin sauki ba tare da doka ta tanka musu ba. Abu na karshe da suke so shine 'wani Buharin.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

"Duk da cewa Buhari zai sauka bayan an zabi wanda zai gaje shi a badi - ko da magajin ya yi bajinta irin yadda Buhari ya yi ko akasin hakan - ya bar babban tarihin da zai wuya wani ya zarce shi wurin aiki:
"Kotu ta kama masu laifi - ba tare da la'akari da kudinsu ko rashinsa ba; dawo da kudaden Najeriya da aka sace aka kai kasashen waje da amfani da shi don inganta rayuwar talakawa; sauye-sauye da suka warware matsalolin da ake fama da su tsawon shekaru kamar rikicin makiyaya da manoma - da yan siyasa suka dade suna amfani da shi don cimma manufarsu; da kare miliyoyin mutane da riga-kafi."

Garba Shehu ya ce wannan kadan ne daga cikin nasarorin Shugaba Buhari. Amma, babban nasararsa shine sauya tunanin al'umma cewa Shugabannin kasa suna neman dare wa kujerar ne don azirta kansu da na kusa da su da kudin talakawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel