Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara

Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya bayyana cewa akwai mutanen da ba zu bari a kawo karshen matsalar tsaro ba
  • Gwamnan yace suna amfani da rashin tsaro wajen sukar gwamnati a wurin yan kasa, domin su samu nasara a siyasance
  • Duk da haka yace ana samun galaba sosai kan yan ta'adda a Zamfara, bayan umarnin shugaban ƙasa

Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace ayyukan ta'addancin yan bindiga ba zai ƙare nan kusa ba a jihar Zamfara sabida wasu yan siyasa.

Gwamnan yace wasu ɗai-ɗaikun yan siyasa a jihar na amfani da matsalar tsaron domin cimma kudirinsu na samun muƙamin siyasa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Matawalle ya yi wannan furucin ne ranar Litinin, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'izar wata mata

Matawalle da shugaba Buhari
Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yace mutanen na amfani da karuwar rashin tsaron wajen shaida wa mutane gazawar gwamnati, don haka ba zasu bari a magance matsalar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane matakai gwamnati ke ɗauka?

Amma duk da haka, Matawalle yace ana samun cigaba a fannin tsaron Zamfara saboda umarnin da shugaban ƙasa ya baiwa hukumomin tsaro, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya musanta rahoton kashe mutum 200 a harin Bukkuyum da Anka, yace mutum 58 ne sarakunan yankin suka tabbatar sun mutu a harin.

Matawalle, wanda ya kai ziyara garuruwan da lamarin ya shafa. yace akwai, "Yan bindigan siyasa," dake ɗaukar nauyin yaɗa alƙaluman ƙarya.

Yaushe tsaro zai dawo jihar Zamfara?

Da aka tambaye shi me ya kamata a yi domin kawo ingantaccen tsaro a jihar Zamfara, gwamnan yace:

"Tun bayan lokacin da na karbi mulki a matsayin gwamna, na yi amfani da hanyoyi da dama domin dawo da tsaro a Zamfara. Da farko mun ɗauki matakin tattaunawar sulhu, kuma sai da muka kwashe wata 9 ba'a kai hari ba."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Abinda Gwamna Masari ya faɗa wa Bola Tinubu kan kawo karshen rikici a jihar Katsina

"Amma abun takaicin sai mutane suka sanya siyasa, suka koma suka faɗa wa yan bindiga cewa gwamnati ba dagaske take ba kan sulhun, saboda ba mu ba su ko sisi ba."
"Wannan dalilin ne yasa na watsar da batun sulhu, amma ya yi aiki na wata 9. Matsalar nan ba zata magantu cikin shekara biyu ba, bayan ta kwashe shekara 8 a baya ana fama da ita, abu ne da za'a bi a hankali."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'iza, sun cinna wa gidan rasuwar wuta

Mutane na tsaka da Jana'izar wata mata, ba zato yan bindiga suka kunno kai, suka bude musu wuta kan mai uwa da wabi.

Ɗaya daga cikin waɗan da suka tsira, yace maharan sun zo kan motocin Sienna guda Bakwai, suka tarwatsa kowa ya nemi hanyar tsira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel