Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya ce Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro da ke gudana a yanzu
  • Mai niyar takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, yayin da ya kai ziyarar jaje jihar Katsina
  • Tinubu ya bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi duk mai yiwuwa domin murkushe miyagun

Babban jagoran jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ce Najeriya za ta yi nasara a yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari kan kashe kwamishinansa, Dr Rabe Nasir da aka yi a kwanan nan, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu
Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu Hoto: The Cable
Asali: Facebook

A cewarsa, kasar na da fadi kuma ta fi karfin wadannan miyagu, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakai domin shafe su.

Tinubu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Lokaci ne mai matukar wahala ga jihar Katsina, domin tana fuskantar matsalolin tsaro da dama. Dan Allah, duk abun da ya samu daya daga cikinmu, toh ya same mu ne mu dukka.
“Mu zamo masu saka ido don taimakawa kasarmu, mu yi wa’azin zaman lafiya da sauya tunanin wadanda suka kuduri aniyar kawo ta’addanci, garkuwa da mutane da munanan ayyuka a tsakaninmu.
"Ina bukatar gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na babban kwamandan rundunar tsaro, ya yi amfani da duk abubuwan da ya kamata domin shafe wadannan mutane.
"Mun raba kuma za mu ci gaba da yin addu'a tare da gwamnatin Katsina da kuma al'ummar jihar don kawar da sharrin garkuwa da mutane da kashe-kashen mutanen da ba su ji ba ba su gani ba."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

A martaninsa, Gwamna Masari ya bayyana cewar matsalar rashin tsaro da ake ciki a jihar ya fara ne daga fashin shanu, wanda ya bayyana a matsayin 'fashin gari', rahoton Premium Times.

Ya ce yan fashin na zaune ne a cikin garin kuma ba daga daji suke kai farmaki ba.

Sai dai ya ce, ana haka ne daji ya zama wajen da miyagu, kamar masu garkuwa da mutane suke boye wadanda suka sace har sai an biya kudin fansarsu.

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

A gefe guda, Tinubu ya ce da gagarumin goyon bayan jama’a, zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci gidan tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja na Ibadan, jaridar The Cable ta rahoto.

Dan siyasar ya ce ya samu martani masu dadi daga manyan masu ruwa da tsaki kan kudirinsa na takarar shugaban kasa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel