‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki gidan wani jami'in dan sanda da ke aiki da rundunar IRT, ASP Aliyu Umar a yankin Kofar Konau da ke Zaria, jihar Kaduna
  • Maharan sun kuma kashe mutum daya yayin da suka harbi wani dattijo a kirji, an gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci
  • ASP Umar ya tabbatar da harin, inda ya ce tawagar tsaro na hadin gwiwa sun yi nasarar kwantar da tarzoman

Kaduna - An tabbatar da mutuwar mutum daya sannan wani ya jikkata bayan 'yan bindiga sun kai farmaki gidan wani jami'in dan sanda da ke aiki da rundunar IRT, ASP Aliyu Umar, a yankin Kofar Konau da ke karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindigar, wadanda suka kai farmaki yankin yan mintoci bayan karfe 9:00 na dare, sun kasance su da yawa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sun yi awon gaba da matan aure da yan mata a sabon harin jihar Kaduna

Sannan kai tsaye suka nufi gidan dan sandan inda suka dunga harbi ba kakkautawa domin tarwatsa mazauna yankin.

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria
‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake magana da jaridar ta wayar tarho, ASP Aliyu Umar, wanda ya tabbatar da harin, ya ce da alama gidansa suka yi nufin kai harin sannan ya ce an kashe wani mai suna Abubakar Aliyu.

Ya kuma ce an harbi wani dattijo mai suna Abubakar a kirji inda aka nufi asibiti dashi cikin gaggawa domin samun kulawar likita.

Ya ce:

"Gidana cike yake da mutane sama da guda 20, ciki harda abokina wanda ya dawo daga Masar, mahaifiyata da ta tsufa da kanne na. Lokacin da naji karar harbi, sai na bude kofar shiga gidana ina tunanin jami'an 'yan sanda ne da ke fatrol, amma sai naga mutane uku rike da bindigogi sannan na gaggauta komawa da rufe kofar."

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

sai dai ya ce matakin da ya dauka bai sa 'yan bindigar sun janye ba yayin da suka farmaki gidansa da alburusai.

"An gode Allah, babu ko mutum daya daga ahlina da lamarin ya shafa. Sai dai an kashe wani Abubakar Sani bayan ya ji rauni daga harbin, yayin da aka harbi wani dattijo Abubakar a kirji kuma an gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci."

Umar ya kara da cewar 'yan bindigar sun kuma sace wasu shanaye da ba a san adadinsu ba mallakar wani makwabcinsa Fulani a wajen kofar Kodak Kona da ke garin Zaria.

A cewarsa, yanzu kura ta lafa a yankin yayin da tawagar tsaro na hadin gwiwa suka kawo masu agaji.

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe mutane a Taraba, suka yiwa mazauna kashedi

A wani labarin, mun ji cewa hankula sun tashi a kauyen Jauro Manu na karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba sakamakon kashe mutane biyar da ‘yan bindiga suka yi.

Kara karanta wannan

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Hakazalika, ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari a wasu karin garuruwa da ke yankin.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa maharan, kimanin su shida sun kai farmaki garin Jauro Manu Sannan suka kashe wani Musa Iraniya, dan kasuwa kuma manomi da misalin karfe 4:30 na yanmacin ranar sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel