Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu ya faɗa wa shugaba Buhari kudirinsa na takara a 2023

Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu ya faɗa wa shugaba Buhari kudirinsa na takara a 2023

  • Jigon APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na takara a 2023
  • A ranar Litinin da muke ciki, Tinubu ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa, inda ya sa labule da shugaba Buhari
  • Wannan na zuwa ne yayin da cece-kuce ya sake barkewa a APC game da saka ranar babban taron jam'iyya na ƙasa

Abuja - Bola Tinubu ya bayyana cewa ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a gidan gwamnatin tarayya, jim kaɗan bayan ganawa da Buhari ranar Litinin.

"Na sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirina, amma ban faɗa wa yan Najeriya ba, har yanzun ina shawari ne," inji shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da Bola Tinubu a Aso Villa

Shugaba Buhari da Tinubu
Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu ya faɗa wa shugaba Buhari kudirinsa na takara a 2023 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Duk da tun baya akwai alamun yana sha'awar kujera lamba ɗaya a Najeriya, Bola Tinubu, ya kauce wa yin kalaman da zasu nuna kudirinsa kai tsaye, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yadda yan Najeriya ke goyon bayan Tinubu

Yayin da kungiyoyin magoya bayansa suka dinga bayyana a kowane ɓangaren kasar nan, jigon na APC ya ƙi fitowa fili ya bayyana kudirinsa.

A watan Oktoba, 2021, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya shiga cikin mambobin APC na yankin Kudu Maso Gabas, suka kaddamar da SWAGA 23, kungiyar yaƙin neman zaben Tinubu.

Wata ɗaya bayan haka, dattijon ƙasa, Tanko Yakasai, yace Tinubu ya zo ya nemi goyon bayansa kan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ƴakasai yace:

"Bana son shiga kowace jam'iyya amma ina da damar nuna goyon baya na ga ɗan takarar da nake so."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da jimamin kashe mutum 200 a Zamfara, Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kudu

"Na faɗi haka a shekarar 1951 cewa ba zan zama mamban wata jam'iyyar siyasa ba, amma zan goyi bayan ɗan takarar da ya kwanta mun a rai."
"Tinubu ya kawo mun ziyara, dama mutum biyu ne na zaɓa, kuma na faɗa duk wanda ya fara neman goyon bayana zan amince masa, Kuma Tinubu ne ya fara zuwa wuri na."

A wani labarin kuma Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20.

Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel