Ta fito fili: Gaskiyar abin da ya kai Goodluck Jonathan wurin shugaba Buhari sau 2 a kwana 7

Ta fito fili: Gaskiyar abin da ya kai Goodluck Jonathan wurin shugaba Buhari sau 2 a kwana 7

  • Sabon rikici na neman barkewa a jam'iyyar APC mai mulki game da ziyarar tsohon shugaban ƙasa Jonathan zuwa wurin Buhari
  • Wasu na kallon abun akwai wata manaƙisa a ƙasa, yayin da wasu ke ganin APC na son tsayar da Jonathan takara ne a 2023
  • Sai dai fadar shugaban ƙasa tace halin da kasar Mali ke ciki ne ke kai Jonathan wurin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Abuja - An samu cece-kuce a jam'iyyar APC mai mulki game da ziyarar tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, wurin shugaba Buhari karo na biyu cikin mako ɗaya.

Ziyarar Jonathan zuwa fadar shugaban ƙasa na zuwa ne yayin da ake yaɗa rahoton cewa wani sashin APC da wasu gwamnoni na son a bashi tikitin takara a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi

Daily Trust ta rahoto cewa tun bayan ziyarar Jonathan ranar Alhamis, 30 ga watan Dusamba, 2021, sabon cece-kuce ya barke tsakanin 'ya'yan APC musamman masu neman takara.

Jonathan da Buhari
Ta fito fili: Gaskiyar abin da ya kai Goodluck Jonathan wurin shugaba Buhari sau 2 a kwana 7 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sai dai a ziyararsa ta baya-bayan nan, Hadimin shugaban ƙasa, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugabannin biyu sun tattauna kan halin da ake ciki a siyasar kasar Mali.

A cewarsa, taron da ECOWAS ta gudanar ranar Lahadi kan yanayin da Mali ke ciki, shi ne musabbabin zuwan Jonathan wurin Buhari.

Suna son mika wa Jonathan tikitin takara ne - TNN

Amma wani jigon APC kuma shugaban kungiyar masoyan Tinubu (TNN), Kunle Okunola, yace bai gamsu da cewa lamarin Mali ke kai Jonatahn wurin Buhari ba.

Ya ƙara da cewa akwai wata makarkashiya da ake kulla wa domin baiwa tsohon shugaban tikitin takara cikin ruwan sanyi a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Shugaba Buhari ya yi magana game da ‘Dan takarar da zai so ya gaje shi a karagar mulki

A cewarsa, hakan ya bayyana ƙarara cewa dalilin kenan da yasa Buhari ya matsa a sake fitar da ɗan takara ta hanyar sasanci a sabon kundin gyaran zabe 2021.

"Ana son kakaba Jonathan ya zama ɗan takara kuma Buhari ba zai iya cewa a'a ba, ina ga wannan ne dalilin da yasa shugaba Buhari ya matsa a saka yarjejeniyar maslaha wajen fitar da ɗan takara a kundin zabe."
"Saboda suna ganin Mista Jonathan ba zai iya fafatawa da Tinubu a zaɓen fidda gwani ba. Dan haka APC na son ɗakko Jonathan ne kawai, babu ko tantama."

Akwai wani abu a kasa

A rahoton Aminiya Hausa, wasu masu sharhi kan siyasa na ganin bayanin halin da Mali ke ciki ne dalilin zuwan Jonathan wurin Buhari ba wani abu bane illa suna son fakewa da lamarin.

A cewar irin waɗan nan manazartan, babu wani abu da zai kai tsohon shugaban zuwa fadar shugaban ƙasa sau biyu a mako ɗaya illa zancen siyasar 2023.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Kazalika, suna ganin maganar Mali za'a iya yin ta ta wayar salula, amma tun da har lamarin ya kai da sun gana to lallai wani abu ne dake bukatar sirri.

A wani labarin na daban kuma Manyan ayyukan raya kasa 10 da gwamnati ta watsar na zunzurutun kudi sama da Tiriliyan N11trn

Daya daga cikin manyan matsalolin ayyukan raya ƙasa a Najeriya shi ne gwamnati na fara su kuma ta watsar da su.

Wasu daga cikin ayyukan sun lakume biliyoyin kudi kuma za su taimaka wajen habbaka tattalin arzikin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel