2023: Shugaba Buhari ya yi magana game da ‘Dan takarar da zai so ya gaje shi a karagar mulki

2023: Shugaba Buhari ya yi magana game da ‘Dan takarar da zai so ya gaje shi a karagar mulki

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi hira ta musamman da ‘yan jarida a tsakiyar makon nan
  • An yi wa Muhammadu Buhari tambayoyi da dama da suka shafi mulki, 2023, matasa da sauransu
  • Da aka tabo batun siyasar 2023, Buhari ya nuna babu ‘dan takarar da ya fifita a zaben shugaban kasa

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai bada takamaimen amsa ba a yayin da aka tambaye shi game da wanda yake so ya zama magajinsa.

Da aka yi hira da Mai grima Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba, 2021 an bijiro masa da maganar wanda yake so ya karbi mulki a 2023.

Legit.ng Hausa ta bibiya wannan hira inda shugaban kasar ya nuna bai da wani ‘dan takara da yake da shi a rai, wanda zai so ya mikawa ragamar mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari zai tattauna da gidajen talabijin na Channels da NTA

Buhari yace bai da ‘dan takara a zabe mai zuwa na 2023, ya kuma ce idan da a ce zai furta gwaninsa a takarar shugaban kasar, ‘dan takarar ba zai kai labari ba.

Daga cikin wadanda ake ganin su na sha’awar neman kujerar shugaban kasa akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da irinsu Bola Ahmed Tinubu.

Shugaba Buhari
Buhari da APC wajen kamfe Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da Shugaba Buhari ya fada

“Ba zan samu ‘dan takarar da na ke so ba, saboda idan na ambaci sunan shi, za a tika shi da kasa.”
“Saboda haka zai fi kyau in bar shi a matsayin sirri domin in cece shi.” – Muhammadu Buhari.

Buhari: Babu abin da ya dame ni da 2023

Jaridar Premium Times ta rahoto shugaba Buhari ya na mai sake tabbatarwa jama'a bai da damar da zai nemi tazarce bayan wa’adinsa sun cika a Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

Buhari ya shaidawa manema labarai cewa babu abin da ya dame shi da batun zaben 2023 domin ba zai yi takara ba, yace siyasar lokacin ba abin da ke gabansa ba ce.

“Siyasar 2023 ba ta cikin abubuwan da ke gaba na.” – Muhammadu Buhari.

Da aka bijiro masa da maganar jam’iyyar PDP mai hamayya da abin da yake fara zuwa masa a rai idan an ambace ta, sai Muhammadu Buhari yace ‘gazawa’.

Kwankwaso ya na nan a PDP

A jiya Laraba ne aka ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tanka masu rade-radin cewa zai bar jam'iyyar hamayya ta PDP, ya sake komawa APC mai mulkin kasa.

Haka zalika tsohon Sanatan Kano ta tsakiya yace zai sanar da jama’a idan ya yanke shawarar neman mulkin Najeriya, yace zuwa yanzu bai tsaida magana ba tukuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel