Manyan ayyukan raya kasa 10 da gwamnati ta watsar na zunzurutun kudi sama da Tiriliyan N11tr

Manyan ayyukan raya kasa 10 da gwamnati ta watsar na zunzurutun kudi sama da Tiriliyan N11tr

  • Daya daga cikin manyan matsalolin ayyukan raya ƙasa a Najeriya shi ne gwamnati na fara su kuma ta watsar da su
  • Wasu daga cikin ayyukan sun lakume biliyoyin kudi kuma za su taimaka wajen habbaka tattalin arzikin ƙasa
  • Mun tattaro muku akalla 10 daga cikin irin waɗan nan ayyukan raya ƙasa, waɗan da aka kwarzanta su lokacin fara wa

Najeriya na da adadi mai yawa na manyan ayyukan da aka watsar, waɗan da gwamnatoci daban-daban suka fara, (Jihohi da FG), sama da shekara 40 da suka shude.

Jaridar Punch ta rahoto cewa jimullan ayyukan da aka fara kuma aka watsar da su a Najeriya ya kai dubu 56,000.

Daga cikin irin waɗan nan ayyukan, akwai wasu guda 10 da ake ganin su ne manya kuma an yi ƙiyasin sun kai darajar tiriliyan N12trn zuwa watan Agusta. 2021.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika
Manyan ayyukan raya kasa 10 da gwamnati ta watsar na zunzurutun kudi sama da Tiriliyan N11tr Hoto: presidency
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tattaro muku waɗan nan ayyuka guda 10 kamar yadda za su zo a ƙasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Kamfanin jirgin sama na Najeriya (Nigerian Airways)

Daya daga cikin ayyukan da Najeriya ke alfahari da su, kamfanin zirga-zirgan jiragen sama, wanda aka fara shi da sunan West African Airways Coorporation Nigeria a shekarar 1958.

Aikin wanda ya lakume bashi da dama, kuma Najeriya ce ke da mallakin kaso mai yawa na aikin, a halin yanzun gwamnati ta watsar da shi.

A shekarar 2019, gwamnatin Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta sanar da shirinta na farfado da muhimmin aikin, har ta canza masa suna zuwa Nigerian Air.

Gwamnatin ta baiwa Danish Consulting Firm kwantiragin aikin sake fasalin tambarinsa, wanda ya lakume dala miliyan ɗaya, amma har yau shiru.

2. Ma'aikatar sarrafa ƙarafa ta Ajaokuta

Gwamnati ta kirkiri ma'aikatar sarrafa ƙarfe wato Ajaokuta Steel Complex a jihar Kogi domin ta zama ƙashin bayan ma'aikatu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

Rahoto ya nuna cewa ma'aikatar ta kai kashi 98 cikin 100 na kammaluwa a shekarar 1994, amma har yanzun babu wani karfe da ta samar bayan an banzatar da aikinta.

Gwamnatin tarayya ta kashe sama da dala biliyan $8bn a kan aikin wanda bai kamata ya wuce dala miliyan $650m ba. Kuma har yanzun aikin bai kammalu ba.

3. Sakateriyar gwamnatin tarayya a Ikoyi

Sakateriyar wacce aka fi sani da suna Federal Secretariat Complex, an fara ta ne lokacin jihar legas ce babban birnin Najeriya.

Babban gini ne mai hawa 15 dake kunshe a abubuwa da dama da kayayyaki a jihar Legas, amma yanzun haka wurin ya koma wurin fasikanci da yan shaye-shaye.

4. Otal na ƙasa da ƙasa a Suleja

Wannan wani aiki ne da labari ya fi yawa a ciki. Gwamnatin jihar Neja ta fara shi a matsayin babban Hotel kuma wurin zuwa shaƙatawa.

Bayan shekaru 39, tsarin ginin Hotel ɗin da aka kafa a farkon ranaku ya fara rubewa yayin da gwamnatoci ke cigaba da zargin juna.

Kara karanta wannan

Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani

5. Babban Hotel a Bayelsa

Aikin gina Hasumiyar Otal din mai hawa 18 ya karbi sunan, "Hasumiyar jayayya' domin ya zama tsuhen husuma da jayayya a jihar Bayelsa.

Marigayi Diepreye Alamieyeseigha, shine ya fara kafa aikin da nufin ya zama cibiyar shaƙatawar mutane daga sassa daban-daban na Najeriya.

Zuwa yanzun, bayan gwamnoni shida sun jagoranci jihar, kuma an batar da biliyoyin naira, aikin bai kama hanyar kammaluwa ba.

6. Hasumiyar Millenium

Aikin gina Hasumiyar Millenium da kuma cibiyar al'adu na ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ake yi tsakiyar birnin Abuja. Mai tsayin mita 170, shi ne gininda ya fi kowane tsayi a Abuja.

Manfredi Nicoletti, shi ne ya zana tsarin ginij da kuma na babban dakin taro na ƙasa Nigeria National Complex, wanda ya kunshi cibiyar al'adu, gini mai hawa 8 da sauran su.

A shekarar 2006 aka fara ginin Hasumiyar kuma an ka tsayin ta ne a 2015 alhalin kuma har yanzuk ba'a kammala ginin cibiyar al'adu ba.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

7. 5-Star Otal a garin Minna

Wannan ginin wanda yanzu haka an banzatar da shi, gwamnatin jihar Neja ce ta fara aikinsa a 2009, yayin da ta yi tunanin gina wani katafaren Otal.

Zuwa yanzun gwamnatin ta kashe miliyan N500m kan aikin amma yana bukatar biliyan N19.6 domin kammala shi baki ɗaya.

8. Otal na ƙasa-da-ƙasa ROC

Gwamnatin jihar Filato ta fara kafa ginin, kuma tarihin wannan aikin ya fara ne tun daga 1981. Manufar aikin shine gina katafaren Otal na alfarma domin masu zuba hannin jari da masu yawon shakatawa.

ROC Otal na nan a Shere Hills, karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, kuma ya cinye hecta 29 na fili.

Otal din mai ɗakuna 318 ya kunshi sashin shugaban ƙasa, sashin kayan hutawa, sashin shugabanni da sauran su.

A tsarin ginin za'a kammala shi a 2011, lokacin da jihar za ta yi bikin murnan cikarta shekara 20, tare da alƙawarin inganta ginin fiye da farko.

Kara karanta wannan

Bangaren Sheikh Gumi ya maida zazzafan martani kan kashe shugabannin yan bindiga a Zamfara

Amma har zuwa yanzun da ginin ya kwashe kusan shekaru 40 babu alamun kammala shi.

9. Filin wasa na Olymfic a jihar Filato

Wannan muhimmin aiki an kafa shi da nufin ya zama tsayayyen filin wasanni wanda zai gogayya da sauran filayen wasa na ƙasa da duniya baki ɗaya.

A lokacin da aka sanya tushen gina filin wasan a 1988, an yi tsammanin zai zama ɗaya tamkar da dubu, amma shekara 32 kenan, har yanzun bai karbi bakuncin ko wasa ɗaya ba.

Jimullan kudi biliyan N7bn gwamnati ta kashe a ginin tun daga 1988 zuwa 2014 kuma har yanzun yana bukatar Biliyan N4bn kafin a kammala shi.

10. Aikin layin dogo a jihar Ribas

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, shi ya fara tunanin gina layin dogo a jihar domin saukaka wa mutane wajen tafiye-tafiye.

Aikin layin dogon wanda aka tsara zai kai tsawon kilomita 12, ya lakume zunzurutun kudi biliyan N50bn, amma gwamnati ta watsar da shi a kilomita 2.6.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin na daban kuma Khadijat yar kimanin shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a zaɓen 2023

A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel