2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

  • Hafizu Kawu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Tarauni a majalisar tarayya, ya ce Osinbajo ne ya dace ya samu mulkin kasar nan bayan Buhari
  • A cewar Kawu, mataimakin shugaban kasan kuma tsohon ubangidansa, ya na da kamala, nagarta da gogewar da ake bukata domin shugabancin kasar nan
  • Kawu ya sanar da manema labarai cewa, hatta Janar Babangida ya ce Farfesa Osinbajo ya fi dacewa ya mulkin kasar nan bayan Buhari

Kano - Kafin zuwan zaben 2023, dan majalisa mai wakilatar mazabar Tarauni a majalisar tarayya na Kano, Hafizu Kawu, ya kwatanta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin mutum mafi dacewa da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Matsayar Kawu na zuwa ne a matsayin abun mamaki ga masu lura da siyasar Kano, tunda ya na daya daga cikin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar wanda ba ya boye goyon bayansa ga takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu
2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga Osinbajo har Tinubu babu daya daga cikinsu da ya bayyana niyyarsa ta fitowa takarar kujerar shugabancin kasa a zaben 2023.

Kawu, wanda tsohon hadimin Osinbajo ne ya sanar da manema labarai a Kano cewa, tsohon ubangidansa ya nuna dukkan cikar kamala da nagartar da ake bukata a tattare da shugaban kasar Najeriya.

"Idan ka na bibiyar wannan al'amari, tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana amincewarsa da Osinbajo kuma ya kwatanta shi da mutumin kirki yayin da wata kungiya mai goyon bayan takarar Osinbajo ta ziyarcesa.
“Idan muka duba wannan bangaren, ina tunanin mutumin da ya fi dacewa ya gaji Buhari shi ne Farfesa Yemi Osinbajo saboda ya na da nagarta da gogewar da ake bukata," yace.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

2023: Gwamnan Arewa yana goyon bayan Osinbajo ya karbi mulki bayan Buhari, ya kawo dalilansa

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya fi cancanta da ya gaji Muhammadu Buhari a 2023.

Daily Trust tace kalaman Gwamnan na jihar Nasarawa sun fito ne kwanaki bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin zai nemi takarar shugaban kasa.

Daily Trust tace kalaman Gwamnan na jihar Nasarawa sun fito ne kwanaki bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin zai nemi takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel