2023: Gwamnan Arewa yana goyon bayan Osinbajo ya karbi mulki bayan Buhari, ya kawo dalilansa

2023: Gwamnan Arewa yana goyon bayan Osinbajo ya karbi mulki bayan Buhari, ya kawo dalilansa

  • Abdullahi Sule yana goyon bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi mulki a 2023
  • Gwamnan Nasarawan yace Mataimakin Shugaban kasan ya dace ya gaji Buhari
  • Progressive Consolidation Group ta shiga Nasarawa, tana yi wa Osinbajo kamfe

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya fi cancanta da ya gaji Muhammadu Buhari a 2023.

Daily Trust tace kalaman Gwamnan na jihar Nasarawa sun fito ne kwanaki bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin zai nemi takarar shugaban kasa.

Da aka yi wani taron kungiyar Progressive Consolidation Group a gidan gwamnatin jihar Nasarawa da ke Lafia, Sule yace Osinbajo ‘dan takara ne mai kyau.

Progressive Consolidation Group tana goyon bayan Yemi Osinbajo ya nemi kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Osinbajo ne ya dace - Sule

“Osinbajo ne ya fi kowa cancanta, kuma shi ne ‘dan takarar da za a iya tallata wa mutane domin ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Mai girma gwamna Sule yana cewa Nasarawa ta na goyon bayan gwamnatin nan ta daure ta yadda mataimakin shugaban kasa zai dare mulki

Sule yace Osinbajo mutum ne mai daraja da kima wanda kowa yake son ya yi alaka da shi A ganinsa, idan Farfesan ya samu mulki, kasar nan za ta cigaba sosai.

Meyasa Progressive Consolidation Group ta ke tare da shi?

Shugaban tafiyar Progressive Consolidation Group, Dr. Aliyu Rabiu, ya yi magana a wajen taron, yace makasudin zuwansu Nasarawa shi ne su yi wa Osinbajo kamfe.

Dr. Rabiu yake cewa manufofi da tsare-tsaren inganta rayuwar marasa galihu da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da su, suna fitar da mutane daga talauci.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Idan har Osinbajo zai yi takara, hakan yana nufin dole uban gidansa, Asiwaju Bola Tinubu ya hakura.

APC ta na neman Jonathan?

Mun ji labari cewa bisa dukkan alamu kusoshin jam’iyyar APC suna zawarcin Goodluck Jonathan, har ana rade-radin za a ba shi takarar shugaban kasa a 2023.

Jigon APC, Salihu Lukman yace PDP ba ta ganin darajar tsohon Shugaban kasa, Dr. Jonathan. Lukman yana ganin Jonathan ya ceci siyasar Najeriya a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel