Wasu jiga-jigai a arewa sun so su hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande

Wasu jiga-jigai a arewa sun so su hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande

  • Bisi Akande, tsohon shugaban APC na rikon kwarya, ya ce akwai wasu manya a arewa da ba su so a tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2015 ba
  • A littafinsa na tarihinsa, Akande ya ce akwai wasu manyan sarakunan gargajiyan daga arewa da su ka ce tsayar da Buhari a matsayin dan takara zai iya janyo matsaloli ga arewa
  • Marubucin ya ce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci kada shugabannin jam’iyyar su kuskura su tsayar da Buhari a matsayin dan takara

Bisi Akande, tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya ya ce akwai wasu shugabannin arewa da su ka nemi kada jam’iyyar ta tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a 2015, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

A littafin tarihin rayuwarsa na “My Participation”, Akande ya ce akwai wasu sanannun shugabannin gargajiya da su ka so a hana tsayar da Buhari a matsayin dan takara don gudun janyo wa arewa matsaloli.

Wasu jiga-jigai a arewa sun so su hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande
Wasu masu fada a ji a arewa sun so hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Marubucin ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nemi shugabannin jam’iyyar APC kada su kuskura su tsayar da Buhari a matsayin dan takara.

Akwai shugaba daga arewa da ya yi kwanaki a Osogbo duk don jan ra’ayin gwamnan jihar

A cewarsa kamar yadda The Cable ta ruwaito, APC ce kawai ta yanke shawarar tsayar da shi takara. Ya kara da cewa:

“Tun farko a bayyane yake, Buhari shi ne zabinmu na shugaban kasa. Hakan ma ya na cikin dalilan da su ka sa aka yi maja.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

“Sai dai an samu takura ko ta ina daga masu ruwa da tsaki, musamman daga arewa, har da shugabannin gargajiya inda su ke matsa mana don kada mu tsayar da shi takarar shugabancin kasa.
“Akwai wani babban shugaba daga arewa da ya yi kwanaki a Osogbo, duk don jan ra’ayin Gwamnan Aregbesola akan kada a tsayar da Buhari takara. Ya ce matsawar mu ka tsayar da shi sai an samu matsala a arewa.
“Mun kuma hadu da Obasanjo inda muka bukaci ya taya mu yakin neman zabe. Amma ya ce ba zai taya mu ba sai dai ya na tausayinmu. A cewarsa ya yanke shawarar kin shiga wata jam’iyya tun da ya bar PDP.”

Mun gano yadda Obasanjo ya dinga wa Buhari zagon-kasa

A boye muka gano cewa ya na ta matsa wa wasu shugabanninmu akan kada su tsayar da Buhari a matsayin dan takara.

Ya kara da cewa an kai wani mataki inda Bola Tinubu ya fuskance shi inda yace masa bai dace ba abinda ya ke yi wa Buhari saboda ya san shi tun a makarantar sojoji.

Kara karanta wannan

Yadda Sambo Dasuki ya roki Tinubu, Akande a ba Buhari takara shekaru 10 da suka wuce

Tinubu ya ce masa mai zai hana ya kira Buhari sannan ya gaya masa ra’ayinsa, daga nan Obasanjo ya ja bakinsa ya yi shiru.

Akande ya kara da cewa abinda ya kara janyo wa jam’iyyar APC farin jini shi ne Buhari. Saboda ya na da kwarjini irin na tsofaffin ‘yan siyasa kamar Obafemi Awolowo, Ahmadu Bello da Nnamdi Azikwe.

Buhari: Bisi Akande Mai Gaskiya Ne, Bai Taɓa Amsa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Cif Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin ma'aikacin gwamnati mai gaskiya da rikon amana, Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda shine babban bako na musamman wurin gabatar da littafi da Bisi Akande ya rubuta kan rayuwarsa ya ce marubucin bai taba sauya halinsa ba tun yana aikin gwamnati da bayan ya gama, na rashin karba ko bada rashawa.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana sirri, ya zayyano yadda Atiku ya nemi sadakan kudi daga Tinubu

Ya karanto daga shafi na 400 a cikin littafin inda Akande ya rubuta cewa bai taba nema ko bada cin hanci ba a rayuwarsa, ya kuma jadada cewa kamilin mutum ne mai gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel