Buhari: Bisi Akande Mai Gaskiya Ne, Bai Taɓa Amsa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba

Buhari: Bisi Akande Mai Gaskiya Ne, Bai Taɓa Amsa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya a matsayin mutum mai gaskiya da amana
  • Buhari wanda shi ne babban bako na musamman a wani taro na kaddamar da littafi mai suna “My Participation”, tarihin Cheif Bisi Akande
  • Marubucin littafin ya bayyana halaye na kwarai wadanda Akande ya ke da dasu yayin da yake ciki da wajen ofishin gwamnatin musamman rashin amsar rashawarsa

Legas - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Cif Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin ma'aikacin gwamnati mai gaskiya da rikon amana, Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda shine babban bako na musamman wurin gabatar da littafi da Bisi Akande ya rubuta kan rayuwarsa ya ce marubucin bai taba sauya halinsa ba tun yana aikin gwamnati da bayan ya gama, na rashin karba ko bada rashawa.

Kara karanta wannan

Ana yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

Buhari: Bisi Akande Mai Gaskiya Ne, Bai Taɓa Karɓa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba
Buhari: Bisi Akande Bai Taɓa Amsa Ko Bayar Da Cin Hanci Ba. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya karanto daga shafi na 400 a cikin littafin inda Akande ya rubuta cewa bai taba nema ko bada cin hanci ba a rayuwarsa, ya kuma jadada cewa kamilin mutum ne mai gaskiya.

Yayin da ya kwatanta shi a matsayin mutumin kirki. Shugaban kasan ya yi wani karin magana na hausawa inda ya ce, “Labarin zuciya a tambayi fuska.”

Mutum ne mai yawan murmushi

Buhari ya kwatanta shi a matsayin mutumin da kullum cikin murmushi ya ke kuma zai iya shiga dawa tare da shi.

Yayin da Buhari ya yi nuni akan tarihin siyasar Akande, musamman lokacin da ya nema zama gwamnan jihar Osun a karo na biyu inda ya ce:

“Sanin kowa ne cewa an cutar da Akande tare da wasu gwmanonin AD, wanda yaudarar da aka yi masa ta dakatar da burinsa na zama gwamna. Asiwaju Bola Tinubu ne kadai ya tsira daga makircin zaben da Shugaba Obasanjo ya shirya.”

Kara karanta wannan

Ba zan bar masu hannu a kisan dalibin kwalejin Dowen, Oromoni, su ci bulus ba, Shugaba Buhari

“Cikin takaici, duk da musulmin kirki ne shi ya amshi kaddararsa ya ci gaba da rayuwa. Ya kuma ci gaba da yi wa kasa bauta.”

Akande ne cikin jajirtattun da su ka shirya majar jam’iyyu don kafa APC

Yayin tunawa da yadda APC ta hau mulki a shekarar 2015, shugaba Buhari ya ce Chief Akande ya na cikin jajirtattun da su ka tsaya tsayin-daka don hada jam’iyyu da dama saboda su tunkude PDP daga mulki.

Buhari ya ce duk da yadda ba su samu nasara ba a takarar da su ka tsaya a 2011 amma jajircewa da sanin mawuyacin halin da PDP za ta jefa kasar nan ya sa su ka yi majar jam’iyyu don dunkulewa wuri guda a 2014.

Ya ce a boye aka zabi Akande a matsayin shugaban jam’iyyar bayan dunkulewarta kuma duk da fadi-tashin da aka dinga, Buhari ya gano Akande mai gaskiya ne.

Kara karanta wannan

Ba dalilin da zai sa APC ta sha ƙasa a zaben 2023 domin yan Najeriya na jin dadin mulkin Buhari, Gwamna

Buhari ya shawarci dalibai akan nazari akan littafin

Don haka Buhari ya bayar da shawarar dalibai su yi nazari akan wannan littafi wanda Dare Babarinsa ya wallafa don su fahimci siyasa.

A cewarsa:

“Dalibai za su karu da wannan littafi musamman a harkar siyasar Najeriya, tsakanin 1999 zuwa 2020.”

A bangaren Cheif Akande, ya yi wa Shugaba Buhari godiya da sauran mutanen da su ka je taron inda ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su hada kai.

Taron ya samu halartar manyan mutane kamar ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu; Ministan cikin gida wanda ya samu wakilcin dansa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan; Sanata Tokunbo Abiru; Sanata Solomon Adeola; Sanata Opeyemi Bamidele; Kakakin Majalisar Wakilai wanda ya samu wakilcin Hon. Enitan Dolapo Badru; Shugaban kwamitin rikon kwaryar APC, Mai Mala-Buni, Dr Usman Bugaje, Sarakuna da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel