Yadda Sambo Dasuki ya roki Tinubu, Akande a ba Buhari takara shekaru 10 da suka wuce

Yadda Sambo Dasuki ya roki Tinubu, Akande a ba Buhari takara shekaru 10 da suka wuce

  • Sambo Dasuki ya yi kokarin ganin Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya tun a zaben 2011
  • Bisi Akande yace Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya nemi su ba Buhari tikitin takarar ACN/CPC
  • Yunkurin hadin-kai bai yiwu ba, a karshe shugaba Goodluck Jonathan ya doke jam’iyyun ACN da CPC

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande ya bayyana yadda Sambo Dasuki, ya huro wuta a kan su ba Muhammadu Buhari takara.

Daily Nigerian ta rahoto Cif Bisi Akande yana cewa tsohon hadimin na Dr. Goodluck Jonathan yana cikin wadanda suka nemi a ba Buhari tuta a 2011.

A littafin na sa, tsohon gwamnan yace Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya hurowa jam’iyyarsu ta ACN a lokacin wuta, ta hada-kai da CPC ta su Buhari.

Hakar tsohon sojan ba ta cin ma ruwa ba domin a karshe hadin-kan bai yiwu ba, kuma Goodluck Jonathan ya yi nasara a zaben shugaban kasan na 2011.

Dattijon yace bayan yunkurin hadewar CPC da ACN ya ci tura, mutane irinsu Babangida da Atiku Abubakar, sun nemi ganin yadda za a shawo kan batun.

Sambo Dasuki
Gwamnatin Buhari ta tsare Sambo Dasuki Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin ya gagara - Akande

“Maganar ta wargaje a lokacin zaben 2011 wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan na PDP ya sake ci.”
“Ya kamata a ambaci kokarin da tsohon mai bada shawara a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) ya yi na zama tsani tsakanin jam’iyyun CPC da ACN.”
“A wancan lokaci, Dasuki yana goyon bayan Buhari ya zama ‘dan takarar shugaban kasa na hadin gamayya. Ya rika zuwa, yana rokonmu, ya na nema masa goyon baya.”
“Ribadu, wanda muka zaba ‘dan takarar shugaban kasa a ACN,yace ya shirya janyewa Buhari. Yace lokacin da ya fito, bai san Buhari na da niyyar takara ba.” - Akande.

Kamar yadda jaridar ta bayyana a wani rahoto da ta fitar, Akande ya yi wannan bayani ne a cikin littafin rayuwarsa da ya rubuta mai suna “My Participations”.

Dabarar da Alkalai su ke yi - Jega

Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega ya ce wasu Alkalai su na saida shari’a a kotu, musamman na harkar zabe sai su yi ritaya domin gudun NJC ta hukunta su.

Farfesa Jega yace da gan-gan aka tsarin lamarin da nufin Alkalai su yi kudi kafin ritaya. Jega ne wanda ya shirya zabukan da aka yi a 2011 da kuma 2015 a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel