APC za ta kora masu riƙe da muƙaman siyasa 7,000 da gwamnanta ya naɗa

APC za ta kora masu riƙe da muƙaman siyasa 7,000 da gwamnanta ya naɗa

  • Jam'iyyar APC mai mulkin kasa reshen jihar Cross Rivers ta yi barazanar korar hadiman Gwamna Ben Ayade su 7,000
  • Sabon shugaban APC na Cross Rivers, Alphonsus Eba, ne ya yi wannan barazanar yana mai cewa har yanzu ba su yi rajista da jam'iyyar ta APC ba
  • A cikin watan Mayun shekarar nan ne Gwamna Ayade ya fice daga PDP ya sauya sheka zuwa APC amma wasu hadimansa har yanzu ba su yi rajitsa da APC ba

Jihar Cross Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Jihar Cross Rivers ta yi barazanar raba hadiman Gwamna Ben Ayade su 7,000 da aikinsu, The Punch ta ruwaito.

Zababen shugaban jam'iyyar a jihar, Alphonsus Eba, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Calabar, babban birnin jihar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

APC ta yi barazanar korar masu riƙe da muƙaman siyasa 7,000 da gwamnanta ya naɗa
APC za ta kori hadiman Gwamna Ayade su 7,000 idan ba su yi rajistan jam'iyya ba kafin karshen 2021. Hoto: Channels TV
Asali: Depositphotos

An bawa hadiman wa'adi zuwa karshen shekarar 2021

Ya ce hadiman gwamnan har yanzu ba su yi rajista ba da jam'iyyar APC kuma ya basu wa'adi zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2021 su yi rajistan idan ba haka ba kuma a kore su daga aiki a ranar 1 ga watan Janairu.

"Ya zama dole a kori dukkan masu rike da mukaman siyasa su 7,000 da ba su riga sun yi rajista da APC ba," a cewarsa.

Ya kara da cewa za a maye gurbin su da mambobin jam'iyyar APC.

Ya ce sashi na 9(5) ta kundin tsarin jam'iyyar APC ya hana nada mutanen da ke wata jam'iyyar daban mukaman siyasa.

Mun fara sulhu da masu korafi a jam'iyyar mu

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da wasu ‘Yan Arewa, ya fadi abin ya ke jira ya ayyana takarar Shugaban kasa

Eba ya ce sabbin shugabannin jam'iyyar da aka zaba sun ziyarci yan jam'iyyar da ke koke kan wasu abubuwa da ke faruwa a jam'iyyar.

Ya ce:

"Mun tattauna da yan jam'iyyar mu da ke korafi. A kidayar karshe da muka yi, mun ziyarci a kalla mambobi 100, sun hada da yara, manya da dattawa. Abin da jam'iyya ta yi imani da shi shine kowa na da muhimmanci."

Ya kuma ce ya yi imani 'karba-karba' ba matsala ne ba a APC, matsalar PDP ne.

Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

A wani labarin, kotun daukaka kara ta sa rabar 16 ga watan Disamban 2021 ta zama ranar sauraron kara don sanin matsaya daga hukunci da babbar kotun FCT wacce ta wofantar da gangamin gundumar Kano na APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta ce mambobin kwamitin shirya gangami ne su ka daukaka karar gaban kotun da ke Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wata takarda wacce kwamishinan labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya saki a ranar Talata, ya ce APC tana jiran jin hukuncin kotun don sanin matakin gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel