Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

  • Kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke ranar 16 ga watan Disamban 2021 a matsayin ranar sauraron karar bangarori biyu na APC din jihar Kano
  • Hedkwatar jam’iyya mai mulki ta ce ‘yan kwamitin gangamin bangarorin jam’iyyar sun garzaya kotun daukaka kara a Abuja ranar Litinin don shigar da kara
  • Kwamishinan labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata, inda yace yanzu haka APC tana jiran sakamakon shari’ar ne

Abuja - Kotun daukaka kara ta sa rabar 16 ga watan Disamban 2021 ta zama ranar sauraron kara don sanin matsaya daga hukunci da babbar kotun FCT wacce ta wofantar da gangamin gundumar Kano na APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

Hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta ce mambobin kwamitin shirya gangami ne su ka daukaka karar gaban kotun da ke Abuja a ranar Litinin.

Ganduje Vs Shekarau: Kotun daukaka kara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zabukan shugabannin APC na Kano
Kotu ta tsayar da ranar sauraron shari'a tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A wata takarda wacce kwamishinan labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya saki a ranar Talata, ya ce APC tana jiran jin hukuncin kotun don sanin matakin gaba.

A cewarsa, jam’iyyar tana son jin matsayar da kotunan zasu tsaya a kai don sanin matakin da za ta dauka a gaba, ana jiran jin hukuncin ranar 16 ga watan Disamban 2021.

Ya ce alamu sun nuna cewa wadanda aka yi kara ba su da masaniya akan karar

Garba ya kara da cewa a batun da aka kawo, APC ta shaida cewa ba a sanar da shugaba da sakataren kwamitin gangamin jam’iyyar ba don ba a sa lambobin wayoyinsu da adireshinsu ba a cikin takardar, duk da dai basu taba haduwa da lauyoyin da aka sa za su wakilce su ba, don haka an tauye musu hakkin ji ta bakunansu.

Kara karanta wannan

Sanusi: Gwamnati ta bayyana mataki na gaba bayan tsohon Sarki ya yi nasara a kan ta a kotu

Kwamishinan ya kara da bayyana yadda shigen lamarin nan ya taba aukuwa da ‘yan kwamitin zartarwa wadanda aka bar su a duhu ba tare da an saurare su ba kuma ba a basu damar tattaunawa da lauyoyin da aka ce su ke wakiltarsu ba.

A cewarsa hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta gabatar da korafin guda biyu gaban kotun daukaka kara, kuma ta bukaci ‘yan jam’iyyar da su kasance masu hakuri kuma masu bin dokokin shari’a.

Hakan ya ci karo da bayanin hedkwatar APC ta kasa

Sai dai hakan ya ci karo da bayanin da hedkwatar APC ta kasa ta saki a ranar Litinin, inda jam’iyyar ta ce har yanzu ba ta samu wani bayani daga shari’ar babbar kotun ba, wacce ta nuna bangaren Sanata Ibrahim Shekarau halastaccen bangare ne.

Sakataren kwamitin rikon kwarya da tsare-tsare, Sanata John James Akpanudoedehe ya fadi hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe

Kamar yadda ya shaida:

“Mu shugabannin jam’iyya na kwarai ne, kuma ba za mu ce komai ba akan shari’ar da ba mu ga sakamakonta ba. Abinda kawai zan ce shi ne zamu nemi ganin asalin takardar shari’ar. Don har yanzu ba mu gani da idanunmu ba.”

Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

A wani labarin, ‘yan kabilar Ibo su na ta ayyuka tukuru don ganin sun samu damar mulkar kasa a shekarar 2023 da ke karatowa.

Yayin da sanannu kuma manyan kasar nan su ke ci gaba da dagewa wurin ganin sun samu hadin kan sauran yankuna.

A ranar Asabar, 4 ga watan Disamba, tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, ya ce a shirye kudu maso gabas take da ta durkusa har kasa don neman goyon bayan sauran yankuna wurin samun damar shugabantar kasa a 2023, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel