Tinubu ya gana da wasu ‘Yan Arewa, ya fadi abinda ya ke jira ya ayyana takarar Shugaban kasa

Tinubu ya gana da wasu ‘Yan Arewa, ya fadi abinda ya ke jira ya ayyana takarar Shugaban kasa

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zauna da ‘Yan Northern Alliance Committee a birnin tarayya Abuja
  • ‘Dan siyasar ya shaidawa kungiyar magoya bayansa cewa ba zai ba su kunya a zabe mai zuwa ba
  • Bola Tinubu yace ya na shawara da mutanensa a kan tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya

Abuja - Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yace ba zai watsawa masu kiran ya yi takarar shugabacin Najeriya kasa a ido ba.

A ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, Daily Trust ta rahoto cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyar Northern Alliance Committee.

An yi wannnan zama ne a birnin tarayya Abuja, inda aka cigaba da kira ga tsohon gwamnan na jihar Legas ya nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Umahi ga IPOB: Kun yi kadan, ba ku isa hana shugaban kasa ziyartar kudu maso gabas ba

Shi kuwa Bola Ahmed Tinubu ya nunawa magoya bayansa cewa zai iya amsa kiraye-kirayen na su.

Ba a ajiye magana ba tukuna - Tinubu

Da yake magana da manema labarai bayan wannan zama jiya, babban ‘dan siyasar ya bayyana cewa har yanzu ya na shawara ne a game da neman takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu
Bola Tinubu da Buhari Hoto: @dailytimesnigeria
Asali: Facebook

Bola Tinubu yace ya na tuntubar abokan tafiyarsa a siyasa domin jin shawararsu a kan neman mulki, yace zai fito da matsayar da ya dauka idan lokaci ya yi.

Jawabin babban jigon na APC

“Ba zan yi watsi da kiran da suke yi mani ba, amma dole in yi shawara da kyau; musamman in zauna da abokai na.”
“Daga nan sai in samu ranar da za mu fito fili, mu fadawa mutanen Najeriya.”
“Amma har yanzu shugaban kasa ya na kan mulki. Ba zan zo in raba masa hankali daga kalubalen da yake fuskanta ba.”

Kara karanta wannan

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

“Saboda za mu tuntubi mutane, kuma mu sanar da mutane manufofinmu. Saboda haka ya rage na ku.” – Bola Tinubu.

Tribune tace shugaban wannan tafiya ta Northern Alliance Committee, Amb. Lawal Mohammed Munir, ya ce zamansu da gwanin na su, ya tafi lafiya kalau.

Ana neman jikawa APC aiki

Wata kungiya ta matasa a jam'iyyar APC, tace ba za ta yiwu mutum ya zama shugaban Jam’iyyar APC da Gwamna a lokaci daya ba, don haka ta kai kara kotu.

Kamar yadda ku ka ji, wannan kungiya ta kai Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni da INEC kara a kotu, tana so a ruguza kwamitin rikon kwarya, a sa ranar yin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel