Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

  • Gabanin zabe a 2023, Gwamna Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana cewa zai koya wa wasu jam’iyyu munanan darrusa
  • Gwamnan na Adamawa ya bayyana hakan ne yayin da yake tabbatar da amincewar taron kansiloli a jihar
  • Fintiri dai dan PDP ne da ya doke Jibrilla Bindow wanda ya gabace shi kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2019

Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ce zai koyar da sauran jam’iyyun siyasa a jihar munanan darrusa a zaben 2023 mai zuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin amincewarsa da kungiyar kansilolin jihar Adamawa a dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola a ranar Laraba 1 ga watan Disamba.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri
Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi, gwamnan Adamawa | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

An jiyo gwamnan jihar Adamawa yana cewa:

Kara karanta wannan

Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya

"Sun gaza a cikin shekaru hudu da suka samu damar gudanar da mulkin jihar, kuma ba za mu bar su su yaudari jama'armu ba, za mu ci gaba da yin aiki tukuru, mu samar da romon dimokuradiyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A kan haka, na yi imanin, za mu koya musu darussa munana cewa za su rasa dukkan zabuka tun daga kan shugaban kasa zuwa matsayi na karshe a cikin al'umma, wato na kansila."

A zaben gwamnan jihar Adamawa na 2019, Fintiri ya samu kuri'u 376,552 inda ya doke Jibrilla Bindow, gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 336,386.

Shugaba na gari muke so ba tare da duba addini da kabila ba, inji Fintiri

A wani lokaci a watan Oktoba, Fintiri ya bayyana cewa, 'yan Najeriya na bukatar shugabanni masu nagarta ba tare da duba kabila ko addininsu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nasarawa: APC bata shirya faduwa a 2023 ba, muna da shiri mai kyau

Channels Tv ta ruwaito shi yana cewa:

“Matsalar Najeriya ba ta tsarin shiyya-shiyya ba ce, ya rage namu mu nemo dan takara mai inganci. Duk inda wannan mutumin ya fito, ba tare da la’akari da addininsa ko kabilarsa ba.
"Abin da ni da ku muke fata a yau shi ne samun shugaba nagari wanda zai iya samar da ci gaban tattalin arzikinmu, tsaro wanda zai yi tasiri ga ci gaban bil'adama, samar da irin kayayyakin more rayuwa da muke bukata."

Atiku zai iya gyara Najeriya, inji Finiri

A bangare guda, Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel