Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya

Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya

  • Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya (NCMPI) ta bukaci a tsayar da dan yankin a matsayin wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • NCMPI ta ce yin hakan zai dawo da zaman lafiya da kuma ci gaba a Najeriya
  • Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, a wani taron gaggawa da ta kira a Jos, jihar Filato

Jihar Filato - Wata kungiyar Musulunci ta arewa ta tsakiya (NCMPI) ta bayyana hanyar dawo da zaman lafiya da kuma ci gaba a Najeriya.

A cewar kungiyar, za a iya cimma hakan ne ta hanyar zabar wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 daga yankin arewa ta tsakiya.

Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya
Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaban NCMPI, Saleh Mandung Zazzaga, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, a taron gaggawa na kungiyar wanda ya gudana a garin Jos, babbar birnin jihar Filato.

Kara karanta wannan

2023: Abin da zai hana mu lashe zaben Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi inji Jigon PDP

Kungiyar ta kira taron ne domin magance rikice-rikicen addini, kabilanci, fadan manoma da makiyaya da sauran matsalolin da yankin ke fada da su, rahoton Daily Trust.

Zazzaga ya yi kira ga kungiyoyi jama’a, na addinai da kungiyoyi masu zaman kansu da su shiga a dama da su a harkar siyasa domin su samu damar bayar da gudunmawarsu wajen yanke hukunci da aiwatar da manufofi a kasar.

Jagoran NCMPI a jahar Kogi, Sani Muhammed Lokoja, y ace kungiyar tana hada kai da kungiyoyin da ba na Musulunci ba da kuma kungiyoyin zamantakewa domin bunkasa zaman lafiya a yankin da ma kasa baki daya, rahoton Independent.

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana cewa maimakon mika tikitin shugaban kasa na 2023 ga wani yanki, kamata yayi a bude shi ga yan Najeriya da suka cancanta.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a wani shirin Daily Politics na Trust TV a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba.

Aliyu ya tuna cewa ya kasance mamba a kwamitin shiya na jam'iyyar PDP wanda yayi rabon kujeru a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel