Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana yiwuwar fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023
  • Fintiri ya ce zai baiwa Atiku goyon baya dari bisa dari idan ya sami tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
  • Gwamnan na jihar Adamawa yace tsohon mataimakin shugaban kasar yana da cancantar da ake bukata wajen tafiyar da mulkin Najeriya yadda ake so

Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa PDP ta koyi darasi, inda ya kara da cewa jam’iyyar a shirye take ta karbi mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce idan aka sake zaben jam’iyyar PDP a matakin tarayya, jam’iyyar za ta yi amfani da gogewar mulkinta na tsawon shekaru 16, sannan za ta yi koyi da kura-kurai da ake zargin APC da aikatawa don samar da kyakkyawan shugabanci da ‘yan Najeriya ke fata.

Gwamna Fintiri ya kuma yi alfahari da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP gabanin zaben mai zuwa.

Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

A wani labarin, jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP ya hana 'yan takara uku tsayawa takarar mukamai a kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Wadanda ba su cancanta ba da mukaman inji PDP sun hada da: Farfesa Wale Oladipo (Osun) wanda ya nuna sha’awarsa ga mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu.

Hakazalika da Okey Muo-Aroh (Anambra) wanda ya nuna sha’awar matsayin Sakataren Kasa Dakta Olafeso Eddy (Ondo) Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel