Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya

Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya sanar da cewa dole ne a ganar da 'yan Najeriya cewa mulkin APC zai iya tarwatsa kasar nan
  • Ayu ya hori kungiyoyi tare da jam'iyyun siyasa kan cewa a wayar da kan 'yan Najeriya saboda jam'iyyar APC ce gagagrumar cutar kansar da ta addabi kasar nan
  • Duk da yace ba shi da matsala da Buhari ko masu taya shi mulki, sai dai zai iya cewa salon mulkinsa da dukkan gwamnoninsa ba shi da kyau

FCT, Abuja - Sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya ce ya dace jam'iyyun siyasa su sanar da 'yan Najeriya cewa karin shekaru takwas na mulkin jam'iyyar APC zai iya kawo tarwatsewar Najeriya baki daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da ya karba wakilan Coalition of United Political Party wadanda suka samu jagorancin Ikenga Ugochinyere har gidansa da ke Abuja.

Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya
Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ayu ya ce akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai wurin kawo karshen APC, wacce ya kwatanta da zama babbar cutar da ke addabar kasar nan.

Ya ce, jam'iyyar siyasa wacce ba ta san me ta ke yi ba ce kawai za ta bar gwamna ya zama shugabanta na rikon kwarya, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce: "Saboda wannan gwamnatin ta zo da farfaganda wacce ta yi amfani da ita wurin kai PDP kasa duk da ayyukan da ta yi wa kasar nan, mu na da babban aiki na ilimantar da 'yan Najeriya kan cewa karin shekaru takwas na gwamnatin nan zai iya zama babbar barna ga kasar nan.
"Hakan zai iya kawo tarwatsewar kasar nan. Don haka duk abinda ya dace ya kamata a yi shi wurin ilimantar da 'yan Najeriya yadda za su bi tsarin damokaradiyya wurin yakice babbar kansar da ke addabar Najeriya a kowanne mataki.

"Hatta gwamnoninsu idan ka duba, su ne mafi tabarbarewa a kasar nan. Ta yaya gwamna zai bar jiharsa tsawon shekaru ya tare a Abuja saboda shine shugaban jam'iyyar siyasa? Wa ke shugabantar jihar ka? Wannan shiririta ce da suke yi.
"Dukkan al'amuransu ba don jama'a suke yi ba. Toh a matsayin ku na kungiyar jam'iyyun siyasa a Najeriya, dole ne ku janyo hankalin 'yan Najeriya. Ina tunanin idan muka yi aiki a matsayin jam'iyyu ba tare da caccakar juna ba, hakan zai fi.
"Ban taba fada da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ko dukkan masu yi masa hidima a Villa. A takaice wasu daga cikinsu duk abokai na ne. Kamar su Farfesa Gambari, ina matukar mutunta shi. Aboki na ne na shekaru amma ya na cikin gwamnati da ba ta yi ba. Me ya ke yi a can? A kan me dan Najeriya mai natsuwa zai kasance a cikinsu?" Ya tambaya.

Sabon Shugaban PDP ya bayyana dabarar da za su bi a kifar da Gwamnatin APC a zaben 2023

A wani labari na daban, Sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi magana game da yadda za su bi wajen karbe mulki a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanata Iyorchia Ayu yana cewa jam’iyyar PDP za ta bi hanyar maslaha domin hada kan ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa.

Wannan dabara ce da jam’iyyar hamayyar za ta bi da nufin kifar da gwamnatin APC a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel