Kasar China ta yi karin haske kan kwace filin jirgin saman Uganda saboda cin bashin $207m

Kasar China ta yi karin haske kan kwace filin jirgin saman Uganda saboda cin bashin $207m

  • A makon da ya gabata ne ake ta cece-kuce kan rahoton cewa China za ta karbe wani filin jirgin kasar Uganda
  • Rahotanni sun ce, kasar China za ta karbe filin jirgin na kasa da kasa daya tilo saboda rancen kudi da Uganda ta karba
  • Sai dai, kasar China ta yi karin haske, ta bayyana cewa, ita ba ta karbe wata kadara BA a madadin kudadenta

Uganda - Hukumomin China sun ce ba su da sha’awar karbe filin jirgin sama na kasa da kasa daya tilo na kasar Uganda, idan kasar ta gaza biyan bashin da China ke binta, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, an amince da bayar da filin jirgin saman Entebbe da wasu kadarorin kasar Uganda ga kasar China a kokarin warware wani rancen kudin da ya kai dala miliyan 200 da Uganda ta ci.

Kara karanta wannan

Beluga, Onavo da wasu kamfanoni 3 da Zuckerberg, mai kamfanin Facebook ya saye

Filin jirgin kasar Uganda na kasa da kasa
Kasar China ta yi karin haske kan batun kwace filin jirgin saman Uganda saboda bashi | Hoto: koko.ng
Asali: UGC

An ce shugaba Yoweri Museveni ya aika tawaga zuwa Beijing, babban birnin kasar China, da fatan sake duba ya zuwa kan batutuwa masu tsauri a rancen.

Rahotanni sun ce, ziyarar ba ta kawo wata nasara ba, yayin da aka ce hukumomin kasar China sun ki amincewa da wani sauyi a ka'idojin yarjejeniyar rancen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A makon da ya gabata, Ministan Kudi na Uganda Matia Kasaija ya nemi afuwar majalisar dokokin kasar saboda "lalata dala miliyan 207" da aka ci daga bankin Exim na China don fadada filin jirgin sama na Entebbe.

Kasaija ya fadawa mambobin kwamitin yayin amsa tambayoyin da 'yan majalisar suka yi cewa:

"Ina neman afuwar cewa bai kamata mu karbi wasu daga cikin sharuddan ba."

Amma da yake mayar da martani kan rahotannin yiwuwar karbe filin jirgin, ofishin jakadancin kasar China da ke Uganda ya ce:

Kara karanta wannan

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

"Zargin da ake yi na cewa 'Uganda ta mika manyan kadarori ga kasar China saboda kudi' ba shi da wata hujja ta gaskiya, kuma kawai niyyar gurbata kyakkyawar alakar da kasar China ke da ita da kasashe masu tasowa ne ciki har da Uganda.
“Babu wani aiki ko guda a Afirka da China ta taba kwacewa saboda rashin biyan bashin China.
“Duk yarjejeniyoyin lamuni da suka hada da na aikin fadada filin jirgin sama na Entebbe, cikin son rai bangarorin biyu suka sanya hannu ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna akan kafa guda ba tare da boye wasu sharuddan siyasa ba.
“Sharuddan yarjejeniyar ba da lamuni na aikin fadadawa da habaka filin jirgin saman Entebbe sun cika ka’idoji da ayyuka da ake yi a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya. Kasar China tana goyon baya kuma tana son ci gaba da kokarin da muke yi na inganta karfin Afirka na samun ci gaba a gida."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jirgin kamfanin Air Nigeria zai fara tashi a shekara mai zuwa

A bangaren gwamnatin Uganda, OpIndia ta ce gwamnatin kasar ta ce bata mika wata kadararta ga kasar China ba.

Da yiwuwar Gwamnatin China ta kwace tashar jirgin saman Uganda saboda gaza biya basussukan da ake binta

Gwamnatin kasar Uganda na gab da rashin babbar tashar jirgin samanta na kasa da kasa sakamakon gaza biyan bashin da ta karba hannun Gwamnatin kasar China.

Tashar jirgin saman mai suna Entebbe International na cikin dukiyoyin da Gwamnatin Uganda ta sanya cikin sharadi yayinda ta karbi bashi hannun China kuma ta amince a kwace tashar idan ta gaza biya.

A cewar rahotanni, Shugaban kasar, Yoweri Museveni, ya tura tawaga birnin Beijing don neman sauki wajen yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel