Babban kuskuren da 'yan Najeriya za su tafka shine su zabi PDP a 2023, jigon APC

Babban kuskuren da 'yan Najeriya za su tafka shine su zabi PDP a 2023, jigon APC

  • Wani jigo a jam'iyyar APC ya bayyana abubuwan da yake gujewa 'yan Najeriya idan suka zabi PDP a 2023
  • Jigon ya bayyana cewa, babban kuskure ne 'yan Najeriya su sake amincewa da PDP ta kara mulkarsu a nan gaba
  • Ya bayyana irin barnar da jam'iyyar PDP tayi a tsawon shekaru 16 na mulkinta, inda yace su suka bata kasar nan

Abuja - Darakta Janar na Voice of Nigeria, Osita Okechukwu, ya ce 'yan Najeriya za su tafka babban kuskure ta hanyar mayar da jam'iyyar adawa ta PDP mulki a 2023.

Ya bayyana cewa PDP ba abar yarda bace don ceto Najeriya saboda masu tallata jam’iyyar suna da sha’awar cin hanci da rashawa da ba za ta iya warkewa ba da kuma tarihin rashin iya tafiyar da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

'Yan APC mashaya barasa ne, su suke sukar ayyuka na a Benue, gwamna Ortom

Okechukwu ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Abuja, ranar Lahadi.

Darakta Janar na VON, Osita Okechukwu
Babban kuskuren da 'yan Najeriya za su yi shine su zabi PDP a 2023, jigon APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya na mai da martani ne kan shirin ceto kasa da jam’iyyar PDP ta ce ta yi ne domin kawar da Najeriya daga matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ta ce gwamnatin APC ta jefa al'ummar kasar a ciki.

Punch ta ruwaito shi yana cewa:

“Ta yaya ‘yan Najeriya za su amince da ‘yar uwar jam'iyyar PDP, ganin cewa magabatanta na cike da gibin amana? Mun san cewa abubuwa na da wuya; Ina ganin gara a bar APC ta gyara Najeriya. Daga ina ake farawa?”

Okechukwu wanda jigo ne a jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta gama farfadowa daga cin zarafi da cin hanci da rashawa da PDP ta jefa kasar a tsawon mulkin ta na shekaru 16.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

Okechukwu ya kuma kara da cewa hukumar EFCC na ci gaba da bincike kan zargin damfarar miliyoyin Naira da wani dan jam’iyyar Kassim Afegbua ya yi kan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da aka tsige.

Ya kuma yi nuni da cewa ‘yan Najeriya ba za su manta da badakalar kudade daban-daban da suka hada da zamba ta Halliburton har zuwa badakalar Dasuki ba.

Okechukwu ya kuma yi tambaya cewa:

“Shin za mu iya mantawa da almubazzaranci da aka yi wa matatun mai na Greenfield na Dala biliyan 23 – daya a Legas, daya a Kogi daya kuma a Bayelsa?

Hakazalika, ya ci gaba da kawo misalai da suke da alaka da cin hanci da rashawa daga mambobi da jiga-jigan jam'iyyar PDP da ta yi mulki a baya.

Sai dai, lokuta da dama Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a 2019 yakan ce shi ne zai iya gyara Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

A wani labarin, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Samuel Ortom ya ce bai so tsayawa takara a zaben 2019 saboda zagin da yake sha daga 'yan adawar sa.

Ortom, wanda aka sake zaba shekaru biyu da suka wuce, ya bayyana hakan a lokacin da ya kaddamar da babban cocin Pentecostal, wani sabon ginin ofishin jakadancin Christian Network a Makurdi, babban birnin jihar.

Ya ce sai da yayi azumin wata uku, inda ya ce ubangiji ya ba shi umarnin sake tsayawa takarar gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel