Limamin Kiristanci ya roki FG da ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu

Limamin Kiristanci ya roki FG da ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu

  • Sunday Onuaha, shugaban limaman cocin Methodists na Umuahia a jihar Abia, ya yi kira ga gwamnati da ta yafe wa Nnamdi Kanu laifukansa
  • Kamar yadda babban faston ya bayyana, ya ce a kasar nan tsintsiya daya ce kuma ana iya bata wa wani rai, amma akwai bukatar yafiya
  • Shugaban cocin Methodist da ke Abuja, ya ce Ubangiji mai rangwame ne kuma cikin rahamarsa zai kawo rangwame kan kalubalen kasar nan

Shugaban Limaman majami'ar Methodist ta Najeriya, Diocese of Umuahia a jihar Abia, Sunday Onuaha, ya ce babu wani wanda ya fi karfin yin kuskure don haka yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yuwuwar sakin shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

Leadership ta ruwaito cewa, shugabannin kabilar Ibo suna ta kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Matashi ya ci A1 8 a jarrabawarsa ta WAEC, yana neman taimako zai karanta likitanci

Limamin Kiristanci ya roki FG da ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu
Limamin Kiristanci ya roki FG da ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

A yayin kara yin kira kan wannan bukatar, Onuoha ya ce Najeriya tsintsiya daya ce inda ya kara da cewa akwai yuwuwar a muzgunawa juna dama, Leadership ta ruwaito hakan.

Shugaban limaman kiristocin ya ce dole ne 'yan kasa su fahimci cewa kasar nan za ta cigaba ne matukar jama'a na neman yafiya kuma ana yafe laifukan juna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin bikin godiya ga Ubangiji kan girbi na shekarar nan da aka yi a Methodist Church Nigeria, Cathedral of Unity da ke Abuja, ya ce:

"Muna da Kiristoci da Musulmi masu yawa kuma suna godiya ga Ubangiji tare da fatan alheri, Ubangiji ba ya barin mutanensa.
"A wannan lokacin, Najeriya na fuskantar kalubale. Mun ratsa lokacin yakin basasa kuma Ubangiji ya tsare mu, zai cigaba da tsare mu kuwa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Shugaban limaman cocin Methodist Cathedral na Abuja, Rabaren Joseph Oche, ya ce:

"Mun san cewa dukkan halin tsananin da muke ciki, wata rana, Ubangiji a rangwamensa da rahamarsa zai kawo mana karshensa saboda babu abinda ya gagaresa. Mun yarda da hakan kuma ina son kuma ku yarda da hakan."

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

A wani labari na daban, kungiyar Arewa Consultative Forum ta dattawan Arewacin Najeriya tace bai dace ayi wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu afuwa ba.

Sakataren yada labarai na kungiyar ACF, Emmanuel Yawe yace ba za a iya yarda da Nnamdi Kanu ba, don haka ya ja-kunne a kan gwamnati ta yafe masa.

Emmanuel Yawe ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar Punch a ranar Litinin. Babban jigon na kungiyar dattawan Arewa yace abin da ya kamata shi ne a bar shari’a tayi aiki tun da gwamnatin Najeriya ta na aiki ne da tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nigeria ya ce jiharsa za ta rika bawa mata N500 idan sun haihu a asibitocin gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel