Sabon Shugaban PDP ya bayyana dabarar da za su bi a kifar da Gwamnatin APC a zaben 2023

Sabon Shugaban PDP ya bayyana dabarar da za su bi a kifar da Gwamnatin APC a zaben 2023

  • Sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, yace za su dage domin su karbe mulki a zaben 2023.
  • Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana haka a lokacin da ya gana da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP daga jihar Benuwai.
  • Ayu yana ganin tsarin maslahar da ta sa ya zama shugaban jam’iyya za tayi aiki wajen yin waje da APC.

FCT, Abuja - Sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi magana game da yadda za su bi wajen karbe mulki a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanata Iyorchia Ayu yana cewa jam’iyyar PDP za ta bi hanyar maslaha domin hada kan ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa.

Wannan dabara ce da jam’iyyar hamayyar za ta bi da nufin kifar da gwamnatin APC a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya tsorata bayan taron gangamin, ya ce Ayu kalubale ne ga APC

Rahoton yace Ayu ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na jiharsa ta Benuwai da suka kada masa kuri’a a Abuja.

Ayu yake cewa tsarin maslaha da aka bi wajen fito da shi a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa ya nuna hakan zai iya hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyyar.

Tsohon shugaban majalisar dattawan yace za a iya bi ta wannan tsari na yin maslaha wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da rigima ba.

“Akwai babban aiki da za mu yi. Kamar yadda muka yi a 1998, za mu sake yin hakan.” – Ayu.

Sabon Shugaban PDP
Taron zaben shugabannin PDP Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Ba zan sauka daga layin gaskiya ba - Ayu

Da yake jawabi, Ayu ya gargadi magautansa cewa ba zai sauka daga akidarsa ta gaskiya ba, yace yana kan layin da gaskiya ta ke, ba tare da nuna son kai ba.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

Haka zalika Sanata Ayu ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka shiga siyasa da nufin samun kudi, su fita daga harkar siyasa, su rungumi kasuwanci.

Jam’iyyar PDP za ta tafi da matasa da mata domin da su za a ci nasara a zabe, a cewar Iyorchia Ayu.

Yekini Nabena ya yi wa Ayu raddi

Sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasan yake cewa zai hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyya kafin 2023. Amma APC mai mulki tace sam hakan ba za taba yiwuwa ba.

Daily Trust ta rahoto Sakataren yada labarai na APC, Yekini Nabena ya yi martani, yace wasu gwamnonin PDP da-dama za su sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

“Wasu gwamnoninsu za su shigo APC. Saboda haka ra’ayinsa ne wannan; amma su tuna cewa ita ma jam’iyyar APC ba barci take yi ba.” - Nabena.

Asali: Legit.ng

Online view pixel