Rikicin APC a Kano: Tsohon mataimakin gwamna Ganduje ya koma tsagin Shekarau

Rikicin APC a Kano: Tsohon mataimakin gwamna Ganduje ya koma tsagin Shekarau

  • Mataimakin gwamna Ganduje a zangon mulkinsa na farko, Farfesa Hafiz Abubakar ya koma tsagin APC na Shekarau
  • A cewarsa ya koma bangaren da gaskiya take ne, kuma yana da yakinin Shekarau ne yake kan gaskiya
  • Hafiz Abubakar ya bar APC ne kafin zaɓen 2019 domin takarar gwamna, inda ya dawo cikinta bayan gaza cimma kudirinsa

Kano - Farfesa Hafiz Abubakar, mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullaji Ganduje, a zangon mulkinsa na farko ya haɗa kai da tsagin Shekarau.

Dailytrust ta rahoto cewa tsohon mataimakin gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne yayin da rikici yaƙi ci yaƙi cinye wa a APC ta jihar.

Shekarau, wanda ya shafe zango biyu a matsayin gwamnan Kano, kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya jagoranci tawagar wasu yan majalisu, inda suka balle daga tsagin Ganduje.

Read also

Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

Rikicin APC a Kano
Rikicin APC a Kano: Tsohon mataimakin gwamna Ganduje ya koma tsagin Shekarau Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Rikicin APC a Kano dai ya jawo zaɓan sabbin shugabanni daga ɓangarorin biyu, Abdullahi Abbas a tsagin Ganduje, da kuma Ahmadu Haruna Danzago a tsagin Shekarau.

Yadda siyasar Farfesa Hafiz ta kasance

Farfesa Hafiz Abubakar, wanda ya yi murabus daga mataimakin Ganduje a 2018 amma daga baya ya sake haɗe wa da shi bayan zaɓen 2019, an hange shi ya halarci taro a gidan Shekarau na Kano.

Hafiz ya fice daga APC da murabus daga mataimakin gwamna domin samun damar tsayawa takarar gwamna ƙarƙashin PDP a zaɓen 2019, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Hakanan kuma baiwa Abba Kabir Yusuf tikitin takarar PDP, Farfesa Hafiz ya fice daga PDP zuwa PRP domin cika burinsa na tsayawa takarar gwamna kuma bai samu ba.

Read also

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Bayan zaɓen 2019 ne kuma Farfesa Hafiz Abubakar ya sake haɗe wa da gwamna Ganduje a jam'iyyar APC, amma yanzun ana ganin sun sake darewa.

Meyasa ya koma tsagin Shekarau?

Da yake zantawa da manema labarai a gidan Sanata Shekarau, ranar Talata, Hafiz Abubakar yace:

"Na haɗa kai na da gaskiya ne wato tsagin Shekarau, saboda suna magana ne kan baiwa kowa hakkinsa da kuma jawo kowa a harkokin siyasan jam'iyya."
"Ina ganin matsayar da Shekarau ke kai itace zata haifar da sakamako mai kyau nan gaba. Ya kamata mu dawo mu tafiyar da jam'iyya yadda ya dace."

A wani labarin kuma Gwamna Bauchi ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace ba su kaunar kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi, yace gwamnatin Najeriya zata iya kawo karshen matsalar tsaro idan ta so.

A cewarsa matukar gwamnati zata iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wurraren da lamarin ya yi kamari, to komai mai sauki ne.

Read also

Siyasar Najeriya: Gwamnan PDP ya yi magana kan shirinsa na komawa jam'iyyar APC

Source: Legit.ng

Online view pixel