Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

  • Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi, yace gwamnatin Najeriya zata iya kawo karshen matsalar tsaro idan ta so
  • A cewarsa matukar gwamnati zata iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wurraren da lamarin ya yi kamari, to komai mai sauki ne
  • Yace mafi yawan laifukan da ake aikata wa ana yin su ne ta hanyar amfani da wayoyin sadarwa na salula

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na da ikon kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin kankanin lokaci idan ta so hakan.

Tribune Online ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da ofishin kungiyar bada horon fasaha NOTAP reshen yankin arewa maso gabas.

Bala Muhammed
Kana da karfin ikon kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya a rana daya idan ka so, Gwamna ga Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wurin taron, wanda ya gudana a Bauchi, Gwamnan yace:

"Idan har gwamnatin tarayya zata iya datse hanyoyin sadarwan wayoyin salula a yankunan ƙasar nan da lamarin ya fi ƙamari, to tabbas zata iya samun nasara kan yaƙi da rashin tsaro da sauran ƙalubale."

Kara karanta wannan

Ku gaggauta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Katsina, Yan majalisa ga Gwamnati

Ta ya gwamnatin zata iya kawo karshen lamarin?

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Usman Tilde, ya cigaba da cewa:

"Mafi yawan manyan laifukan da ake aikata wa ana yin su ne ta hanyar kiran wayar salula. Tattaunawa kan kuɗin fansa da sauransu, saboda haka idan aka datse sabis abun zai zo ƙarshe."

Gwamnan yace duk da hanyoyin sadarwa sun zo da cigaba sosai, amma amfani da su ta hanyar da bata dace ba yasa matsalolin da suke haifarsa ya fi cigaba a Najeriya.

Ya kara da cewa mafi yawan manyan ayyukan ta'addanci da ake aikata wa yanzun a Najeriya yana faruwa ne ta hanyar amfani da sadarwa.

"Ya kamata mu ɗauki matakin ko wane irin hali zamu shiga domin kare rayukan yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba, waɗan da yan bindiga suka matsa wa lamba."

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Gwamnan ya yaba wa NOTAP

Daga nan kuma, gwamnan ya yaba wa NOTAP bisa namijin kokarin da suke wajen horar wa da kuma habbaka fasaha a faɗin Najeriya.

A cewarsa abinda ƙungiyar take yi yana taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba ta bangaren fasaha a ƙasa.

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

A ranar Jumu'a da ta gabata, 12 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin siyar da gidajen da ta gina ga yan Najeriya a farashi mai rahusa.

Gwamnatin ta bude sabon shafin yanar gizo domin mutane su nemi siyan ɗaya daga cikin gidajen kai tsaye daga inda suke.Mun tattara muku jerin hanyoyin da zaku bi, ku cike bayanan ku a wannan shafin domin amfana da shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel