Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

  • A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood
  • Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau
  • Hakanan kuma akwai karin bayani kan sabon ɗakin taro da Jaruma Daso ta bude a birnin Kano

Kano - Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa guda 5 da suka faru a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood cikin mako daya da ya gabata.

Jaridar Aminiya Hausa ta rahoto cewa Kannywood na ɗaya daga cikin masana'antun dake jan hankalin mutane musamman a arewa.

Kannywood
Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood Hoto: @rahamasadau
Asali: Instagram

Ga su kamar haka:

1. Sabon fim ɗin sarki goma ya tara miliyoyi

Sabon shirin fim mai suna sarki goma zamani goma ya tara makudan kudade da suka kai miliyoyin nairori daga fara haska shi a gidan Sinima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fim din wanda ya samu shiryawa daga babban furodusa, Abubakar Mai Shadda, kuma Jarumi Ali Nuhu ya bada umarni ya haɗa kimanin miliyan N3,707,500.

Daga cikin hazikan jaruman da suka nuna bajintarsu a fim ɗin akwai, Momee Gombe, Maryam Yahaya, Umar M Shariff, Shamsu Dan-Iya da sauransu.

2. An tuna da marigayi Isiyaku Forest

Masana'antar Kannywood ta tuna da marigayi Isiyaku Forest, ta hanyar yin rubutu da kuma dora hotonsa a kafar sada zumunta.

Malam Yala, shine ya tuna da marigayin, inda ya saka hotonsa tare da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tare da kara masa addu'an neman rahama ga Ubangiji.

3. Zango na da biyayya ga mahaifiya

Jamilu Kochila yace jarumi Adam A Zango yana da matukar kokari wajen biyayya ga mahifiyarsa da kuma ba ta tsantsar kulawa.

Adam A Zango
Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood Hoto: Official Adam Zango
Asali: Instagram

Kochila yace:

"In dai ta bangaren biyayya ga mahifiya ne da kyautata mata to ka dace abokina, ni shaida ne, Allah ya raba ku lafiya."

A makon da ya gabata ne Jarumin ya sanya wa ɗiyarsa da aka haifa masa sunan mahifiyarsa kuma ya tabbatar da haka a shafinsa.

4. Daso ta bude sabon dakin taro

Jaruma Saratu Gidado, wacce mutanen dake bibiyar Kannywood suka fi sani da Daso, ta bude sabon ɗakin taro na biki ko suna a Kano.

Bugu da ƙari, Jaruma Daso ta rada wa wurin suna 'Daso Event Center' bayan bikin da ta shirya na bude wurin.

Daga cikin manyan jaruman da suka halarci bikin akwai, Dauda Kahutu Rarara. Nura M Inuwa, Rukayya Dawayya.

Shin Rahama Sadau ta koma Kannywood?

Legit.ng Hausa ta gano cewa a halin yanzun Rahama Sadau na can jahar Adamawa inda ake ɗaukar wani fim da zata fito a ciki.

Fim ɗin mai suna 'Gambo da Sambo' ya tara jarumai irinsu, Sani Danja, Rahama Sadau, Daushe da dai sauransu.

A wani labarin kuma mun haɗa muku Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood Indiya

Tun a baya dai Sadau ta buga hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Rahama Sadau, ta saba jawo cece kuce kan shigar da bata dace da addininta ba kuma ta dora a kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel