Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

  • Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila yace ya kamata APC tayi izina daga zaben da aka yi a Anambra
  • ‘Dan siyasar yana ganin zaben gwamnan jihar Anambra darasi ne ga jam’iyyarsu ta APC mai mulki
  • Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa sakamakon zaben ya nuna an bar lokacin karfa-karfa

Abuja - Tsohon mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar majalisa, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya tofa albarkacin bakinsa game da zaben Anambra.

Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi jawabi a shafin Facebook a karshen makon da ya wuce, yana kira ga APC ta dauki darasi a zaben gwamnan jihar.

Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya tabar wakiltar Takai da Sumaila a majalisar tarayya yace an wuce lokacin da za a rika kakaba ‘yan takara da karfi da yaji.

Daily Trust ta tsakuro jawabin da ‘dan siyasar na jihar Kano yayi, inda ya tabo batun rikicin cikin gidan da ake fama da shi a jam’iyyun APC mai mulki da PDP.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1

A cewar Kawu Sumaila, PDP da APC duk suna cikin matsaloli, sai dai a cewarsa APC ta shawo kan sabanin da ya bijiro mata saboda tana da shugaban kasa.

Tsohon Hadimin Buhari
Abdurrahman Sulaiman Kawu Sumaila Hoto: @HonKawuSumaila
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi magana

“Amma mu fadawa kan mu gaskiya, mu shirya yi wa juna adalci a APC. Lokacin da za a kakaba ‘yan takara ya wuce.”
Zaben Anambra ne babban darasin da za mu dauka.” – Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila.

Independent tace Sumaila ya nuna cewa bai damu da yadda jam’iyyu suka bi wajen fito da ‘yan takararsu ba, ganin majalisa tayi wa dokokin zaben kasa gyara.

“PDP tana fuskantar rashin dadin adawa, irin wanda mu ka sha na kusan shekaru 16, mun fi samun matsaloli a jam’iyyar APC.”
“Amma tun da muna da shugaban kasa, mun shawo kan na mu. Ina tausayin APC a ce ba ta da kujerar Shugaban kasa.” - Sumaila.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

APC tana zawarcin gwamnan PDP?

Kwanaki aka ji shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kai ziyara Abia, har an ba shi sarauta a Aba. A nan ya yi wa Gwamnan Abia tayin dawowa APC.

A shekarar nan, APC ta janyo Gwamnonin PDP har uku; Ben Ayade, Dave Umahi da Bello Matawalle. Ahmad Lawan zai so a ce Victor Ikpeazu ya bi sahunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel