Siyasar Najeriya: Gwamnan PDP ya yi magana kan shirinsa na komawa jam'iyyar APC

Siyasar Najeriya: Gwamnan PDP ya yi magana kan shirinsa na komawa jam'iyyar APC

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo yace ba shi da wani shirin sauya jam'iyyar siyasa daga PDP da yake ciki
  • A cewar gwamnan, jihar Edo ta shiga wani kangi na kwan gaba kwan baya a cigaba shekaru biyar da suka wuce, amma yanzun ta koma dai-dai
  • Tsohon shugaban APC na ƙasa, John Oyegun, ya yaba wa gwamnan bisa namijin kokarinsa wajen shawo kan matsalar matasa dake ƙaura

Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, yace a halin yanzu ba shi da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar PDP ya koma wata j'iyya.

Tribune Online ta rahoto cewa Obaseki ya yi wannan furuci ne a Benin City, a wani ɓangare na taron Alaghodaro na wannna shekarar.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Shugaba Buhari na da hakuri wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya, Dan majalisa

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tukuru wajen kawo cigaba a faɗin jihar Edo, ta yadda mazauna jihar zasu rayu cikin walwala da jin daɗi.

Godwin Obaseki
Siyasar Najeriya: Gwamnan PDP ya yi magana kan shirinsa na komawa jam'iyyar APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A jawabin gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wata matsin lamba da za'a mun na sauya sheka, ba inda zan je, zan cigaba da jagorancin mutanen jahar Edo yadda ya kamata. Bama bukatar komawa wata jam'iyya don gyara Edo."
"Fatan mu shine mu ɗaga Edo zuwa matakin da ya dace, domin an kirkiri jihar mu ne domin ta samar da jagoranci mai kyau a ƙasa, wannan ita ce jihar mu, kuma haka zata cigaba."

Zamu kimtsa matasa domin gobe - Obaseki

Gwamnan yace wannan taron ya zama wani ginshiki da gwamnatinsa take amfani da shi wajen shirya matasa domin su ne jagororin gobe.

"Zamu cigaba da yin bakin iyawar mu a gwamnatance domin inganta rayuwar mutanen mu, waɗan da suka damƙa mana amanar shugabanci da kuri'unsu."

Kara karanta wannan

Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo

"A shekaru 5 da suka shuɗe, mun shiga wani ƙangi a bangaren cigaban jahar Edo, amma wannan lokaci ya wuce, yanzun muna samun cigaba sosai."

An yaba wa gwamna Obaseki

Da yake nasa jawabin, tsohon shugaban APC na ƙasa, John Oyegun, ya yaba wa gwamna Obaseki bisa shawo kan ƙaurar mutane a jihar.

The Cable ta rahoto Oyegun yace:

"Yanzun mun wayi gari matasan mu ba sa tsere wa ta cikin tafkin ruwa saboda kokarin da ka yi na shawo kan matsalar. Yanzun matasan na shirya kan su saboda gobe."

A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yaceɓyanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya.

Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya sallami shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel