Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo

Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi hannunka mai sanda ga 'yan siyasar da ke daukarwa talakawansu alkawara a lokacin kamfen ba tare da cikawa ba
  • Shaibu ya bayyana shi ya sha banban da irin wadannan yan siyasa, domin baya fadin karya don a dama da shi a cikin jama'a
  • Ya ce shi mutum ne mai sanya Allah a cikin dukkan lamuran da ya sanya a gaba

Benin, Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya bayyana cewa wasu yan siyasa sun yarda da fadar karya don kawai a dama da su a cikin jama’a.

Shaibu ya bayyana hakan a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, a Benin, babbar birnin jihar, lokacin da ya wakilci Gwamna Godwin Obaseki wajen kaddamar da makarantar firamare na Adesuwa a barikin yan sanda, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo
Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo Hoto: Philip Shaibu
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ni dan siyasa ne na daban, ni dan siyasa ne da ke ganin fuskar Allah a komai da nake yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ni ba dan siyasa da ya yarda da fadar karya don ci gaba da yin tasiri a cikin al’umma bane kuma wannan shine abun da muke kokarin kawarwa a jihar Edo.
“Wasu mutane na buga siyasa da harkar ilimi, wasu mutane a lokacin kamfen sun ce za su bayar da ilimi kyauta, amma da zaran sun kai wajen sannan suka ga zahiri, sai su zo su fada maka cewa alkawari ne kawai.”

A wani labarin na daban, tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana, yace ya kamata yan Najeriya su canza shugabanni da jam'iyyun siyasar da basu taɓuka komai a zaɓen 2023, kamar yadda This Day Live ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sai anyi tsarin yaki da rashawa na gaba-gadi kafin Najeriya ta tsira, Sanata Ndume

A cewarsa, maimakon da nasani da bacin rai, kamata yayi yan Najeriya su saurari lokacin da ya dace a babban zaɓen dake tafe don hukunta shugabannin da suka gaza cika alkawurransu.

Gana ya faɗi haka ne a wata fira da manema labarai jim kaɗan bayan kaddamar da sabuwar cocin Anglican a Zone 5, Wuse Abuja, ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel