Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace yanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya
  • Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC
  • Tsohon sanatan ya ƙara da cewa ba shi da tunanin ficewa daga PDP domin kawai ba'a bashi tikitin takara ba a 2023

Abuja - Tsohon shuagaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yace a wurinsa baya kallon siyasa a bukatun karan kansa kaɗai.

Dailytrust tace Saraki ya faɗi haka ne yayin da yake bada amsa kan ko zai fice daga PDP matuƙar ba ta bashi tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023.

Sanata Saraki yace ya fi maida hankali wurin ganin Najeriya ta dawo kan hanya mai kyau da kuma samun cigaba a ƙasa.

Read also

Ni zan karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023, Gwamna

Bukola Saraki
Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Tsohon gwamnan jihar Kwara, wanda ake jita-jitar yana sha'awar takarar shugaban kasa, ya yi alkawarin taimakawa duk wanda PDP ta tsayar takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon sanatan ya yi wannan furuci ne yayin da yake fira da kafar watsa labarai ta Arise TV.

Me Sanata Saraki yake bukata a 2023?

Saraki ya ƙara da cewa mafi yawan yan Najeriya ba su jin daɗin yanayin da ƙasar nan take ciki a yanzun.

Yace yanzun fatansa shine yadda za'a gyara PDP domin ta ƙalubalanci jam'iyyar APC kuma ta samu nasara.

Saraki yace:

"Game da tambayar idan ban samu tikiti ba, zan sauya sheka? Idan baku mance ba na nemi takara a 2019 amma ban samu ba, daga nan sai na koma na taimakawa Atiku Abubakar."
"Ni mamba ne a cikin tawaga, bukatun kai na ba su ne damuwa ta ba a yanzu, abinda ya fi amfani shine mu ceto Najeriya."

Read also

Wani babban Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya fice daga cikin jam'iyyar, ya bayyana dalilai

"Ina da ƴaƴa da jikoki, saboda haka wajibi ne mu samar da ayyukan yi a ƙasa ko dan gyara rayuwar matasan mu. Maganar gaskiya dan kunga wasu na sauya sheƙa ba shi zaisa nima na sauya ba."

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan APC tare da dubbannin magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Benuwai.

Sanata Abba Moro, yace jam'iyyar PDP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya daga halin da APC ta jefa ta idan ta samu dama a 2023.

Sanatan, wanda ya yi jawabi wajen bikin tarbar masu sauya sheƙan, yace Najeriya ta rasa komai ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Source: Legit.ng News

Online view pixel