Bakano ya bayyana dalilin da yasa yakeson zama shugaban matan jam'iyyar APC

Bakano ya bayyana dalilin da yasa yakeson zama shugaban matan jam'iyyar APC

  • Wani matashi mai shekaru 26 ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban mata a jam'iyyar APC
  • A wata hira da aka yi dashi, ya bayyana dalilin da yasa ya zabi tsayawa takara a kujerar da mata ke tsayawa
  • Ya ce a ransa yana son taimakawa mata, wannan yasa yake son tsayawa takara domin jagorantarsu

Kano - Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, wani matashi dan shekara 26 mai suna Ameer Sarkee a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce ya tsaya takarar shugabancin mata na kasa ne saboda a ko da yaushe yana son taimakawa mata.

A cewersa tun yana karamin yaro yake aikin taimakawa matan da ya hadu dasu masu neman taimakon gaggawa.

Dan takarar kujerar shugaban mata a APC | Hoto: bbc.com
Bakano ya bayyana dalilin da yasa yakeson zama shugaban matan jam'iyyar APC
Asali: UGC

Da yake bayyana yadda yake taimakawa mata ga BBC Hausa, ya ce tun yana karami yake taimakawa:

Kara karanta wannan

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

" Kamar daukar kaya ko sayo musu wani abu - kuma hakan ne ya sa nake son zama shugaban mata na jam'iyyarmu."

Wannan ba shi ne karon farko da Sarkee ya nemi wani matsayi na musamman da aka kebe don mace ba. A 2019, ya tsaya takarar shugabancin mata a kungiyar Kwankwasiyya ta mabiya Kwankwaso. Kungiyar tana da mabiya da yawa a cikin jam’iyyar adawa ta PDP.

Ameer wanda ya kammala Kwalejin Kimiyya ta jihar Kano ya sha kaye a wancan karon.

Ba a bayyana lokacin da Ameer ya koma APC ba. Sai dai ya ce ba zai bari a yi galaba a kansa ba a wannan karon, yana mai cewa yana da gogewa wajen tunkarar matsalolin mata.

Ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da an kara jin muryoyin mata a siyasa da mulki idan ya zama shugaban mata na kasa a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Ya bayyana dalilinsa da cewa, ai ubangiji ya halicci maza ne domin su jagoranci lamurran mata, don haka yake son yi musu jagoranci mai inganci.

Ameer ya ce yana fatan matan jam’iyyar APC za su amince su zabe shi duk da cewa shi namiji ne, inda ya ce babban kalubalen da yake fuskanta shi ne matan da suke ganin ya kwace musu damarsu.

Sabanin fargabar da ya ke da ita, Ameer ya ce, yayin da yake fuskantar kalubale na samun karbuwa daga wasu mata, wasu kuma na tunkararsa a matsayin shugaban mata na jam’iyyar APC na kasa.

A bangaren rayuwarsa, har yanzu Ameer bai yi aure ba amma yana shirin yin hakan tare da burinsa na jagorantar mata a jam'iyyar da ke mulkin Najeriya.

PDP ta yi ittifaki kan Ayu Iyiorcha matsayin sabon shugabanta gabanin taron gangaminta

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin jam'iyar PDP, gabanin babban taron ta na kasa na ranar 31 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Fitowar Ayu ya biyo bayan awanni na ci gaba da tarurrukan da masu ruwa da tsaki na PDP na Arewa ke yi a Abuja cikin awanni 72 da suka gabata.

An zabi Ayu ne bayan cin nasara kan wasu 'yan takara biyu; tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema da Sanata Abdul Ningi, inji Rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel