Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

  • Matasa a jihar Benue sun caccaki gwamna, inda suka bayyana shi a matsayin mai kokawa kan zargin da ba gaskiya ba
  • Sun ce ya kamata gwamnan ya daina kokawa kan yadda Buhari ke gudanar da mulki ya natsu ya yi wa mutanensa aiki
  • Hakazalika, sun caccake shi kan cewa, ya kamata ya kokarta biyan ma'aikata kudadensu na albashi da fanso

Benue - Wata fitacciyar kungiya a jihar Benue mai suna ‘Tiv Youth Council Worldwide’ ta caccaki gwamna Ortom kan yadda yake sukar shugaba Buhari a koda yaushe.

Kungiyar ta bayyana cewa yayin da Ortom ke sukar shugaban a koda yaushe, al’ummar Binuwai suna shan wahala matuka a karkashin mulkinsa.

Kungiyar matasan ta kuma zargi gwamnan da kin biyan ma’aikata albashi da kudaden fansho, balle a ci gaba da bunkasa jihar ta fuskoki da yawa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom | Hoto channelstv.com
Asali: UGC

Kungiyar matasa ta 'Tiv Youth Council Worldwide' ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Samuel Ortom za ta zama mafi muni a tarihin jihar Benue kuma za ta kasance mafi duhu a daukacin shekarun da jihar ta yi.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman gwamna Ortom na cewa gwamnatin Buhari ta fi gwamnatocin soja da suka shude a Najeriya muni.

Ta bayyana haka ne cikin sanarwa mai hannun shugaban kungiyar matasan Tiv Hon. Mike Msuaan da aka aika wa Legit.ng a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana cewa, maimakon gina hadin kan da ake bukata kamar sauran gwamnoni da gwamnatin tarayya, Gwamna Ortom ya ci gaba da zarge-zarge kan wasu.

Wasan suka daga gwamna Ortom

Kungiyar ta zargi gwamnan jihar Benue da yin rufa-rufa da rashin gaskiya ta hanyar bata sunan shugaba Buhari a ko da yaushe.

Kara karanta wannan

Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara

Wani bangare na sanarwar ya bayyana yadda gwamnan yake bijiro da dalilai da suke hanashi tun hawansa na farko a 2015.

A yanzu kuwa, sanarwar ta ce Ortom na amfani da sukar Buhari domin kaucewa yiwa mutanensa aiki da ciyar da jihar gaba.

Sanarwar ta ce:

“Da farko, ya zargi magabacinsa Sanata Gabriel Suswam da karkatar da kudaden jihar da aka tanada domin aikin ci gaba. Ya kafa wani kwamitin shari’a karkashin jagorancin mai shari’a Kpojime domin ya binciki Suswam.
“Kwamitin ya tuhumi tsohon gwamnan da sace zunzurutun kudi har biliyan 107. A cewar Ortom, yana bukatar Suswam ya mayar masa da biliyan 60 kawai domin mayar da jihar Benue zuwa Landan.
“Gwamna Ortom ya zargi karancin kudade da rashin iya biyan albashin ma’aikata, fansho ko kuma gudanar da duk wani aikin raya jiha. Ya ci gaba da tsalle daga wasan zargin nan zuwa wancan.
“Mafi ban dariya shi ne da’awarsa da ya yi cewa ya kori aljanun da ke da alhakin gazawarsa. A yau ya dora laifin rashin tsaro da gazawarsa”.

Kara karanta wannan

Mafi munin mulkin soja da aka taba yi a Najeriya yafi gwamnatin Buhari walwala da jin daɗi, Ortom

Gwamnan Benue mafi muni da aka taba yi

Kungiyar ta kara da cewa Ortom na gab da kafa tarihi a matsayin gwamnan Benue mafi muni da aka taba yi.

Mafi muni a cikin mulkin soja ya fi saki a kan gwamnatin shugaba Buhari da APC, Gwamna Ortom

A baya, Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya sake sukar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ortom ya yi ikirarin cewa duk lalacewar gwamnatin sojoji ta fi mulkin yanzu karkashin jam'iyyar APC sauki da jin dadi.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Makurdi, jim kadan bayan dawowarsa daga ganganmin PDP na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel