Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

  • Wani sabon bayani ya billo kan kisan babban sojin sama mai murabus, AVM Muhammad Maisaka, da aka yi a safiyar yau Talata
  • Wani makwabcin marigayin, Abubakar Gwantu ya bayyana cewa makasa da aka yo haya ne suka kashe marigayin ba wai yan bindiga ba
  • Gwantu ya bayyana cewa Maisaka ya dade baya fita domin yana fama da cutar shanyewar barin jiki

Jihar Kaduna - Sabbin bayanai sun bayyana kan yadda aka halaka babban jami’in soja mai ritaya a Kaduna a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.

Wata majiya ta kusa da iyalan marigayi AVM Mohammed Maisaka, Abubakar Gwantu ya ce kisan na iya zama abun da aka kitsa, Vanguard ta rahoto.

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi
Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Rahoton ya kuma kawo cewa makwabcin nasa ya kuma bayyana cewa Maisaka ya dade baya fita saboda jinya da yake yi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Maharan dauke da makami sun isa gidan Maisaka a daren jiya Litinin inda suka hadu da shi da matarsa a falo sannan suka harbe shi har lahira.
"Maisaka na fama da cutar shanyewar barin jiki sakamakon rashin lafiya da yayi na tsawon shekaru uku kuma yana kan jinya ne har zuwa mutuwarsa.
"Shakka babu duk wanda ya aikata masa haka yana da wani daddan gaba a kan shi, saboda Maisaka ya dade baya yawo, illa kawai ya je kasar waje yin magani, yana jinya a gida sai kuma idan ya je ganin likita a asibitin gida idan bukatar hakan ta taso.
"Duk da adawar iyalinsa, ya gina wani asibiti mai zaman kansa a yankin Rigasa, Kaduna saboda son da yake yi wa ayyukan jin kai. Duk da matsayinsa da kuma gatarsa, ya ki zama a wajen garin inda a nan ne ya gina gidansa bayan ritaya.

Kara karanta wannan

Rushewar Ginin Legas: Sun hanani aiki a wajen don ni Musulmi ne, bayan awa biyu ginin ya rushe

"Duk da haka, Allah shi ya san daidai. Allah ya karbi shahadarsa ya saka masa da Aljannah."

'Yan bindiga sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka tare da jikansa a Kaduna

Da farko mun kawo cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da kisan babban sojin sama mai murabus, AVM Muhammad Maisaka, da ‘yan bindiga su ka yi a gidansa da ke Rigasa, karamar hukumar Igabi da ke jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito yadda jami’in hulda da jama’an rundunar na jihar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar wa da NAN aukuwar lamarin ranar Talata a Kaduna.

Jalige ya bayyana yadda lamarin ya faru da safiyar Talata, sannan har mai gadin gidansa ma ya raunana sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel