Mafi muni a cikin mulkin soja ya fi sauki a kan gwamnatin shugaba Buhari da APC, Gwamna Ortom

Mafi muni a cikin mulkin soja ya fi sauki a kan gwamnatin shugaba Buhari da APC, Gwamna Ortom

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya bayyana cewa bai taba ganin mulki irin wannan na jam'iyyar APC ba
  • A cewarsa mafi muni a cikin mulkin soja da Najeriya ta yi fama da shi a tarihi, ya fi gwamnatin shugaba Buhari sauki ga yan Najeriya
  • Yace babu makawa jam'iyyarsa ta PDP zata karbi mulki a babban zaɓen 2023 saboda gazawar APC ta kowane ɓangare

Benue - Gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom, ya sake sukar gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ortom ya yi ikirarin cewa duk lalacewar gwamnatin sojoji ta fi mulkin yanzu ƙarƙashin jam'iyyar APC sauki da jin daɗi.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Makurɗi, jim kaɗan bayan dawowarsa daga ganganmin PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Shugaba Buhari da Ortom
Mafi muni a cikin mulkin soja ya fi sauki a kan gwamnan shugaba Buhari da APC, Gwamna Ortom Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na samu damar karanta tarihin Najeriya da waɗanda suka lalata mana ƙasa, har da zamanin mulkin sojoji. Mun saba cewa duk lalacewar mulkin farar hula ya fi na soja."
"Amma saboda mulkin APC, ina mai bayyana cewa mafi lalacewar mulkin soji da muka samu a Najeriya yafi wannan gwamnatin karkashin APC.
"Ban taba ganin irin haka ba, mutane ba su ƙaunar gaskiya kuma ba su son a basu shawara. Sai su canza komai su shaida wa duniya kana yaƙarsu ne, wai ba mulkin demokaradiyya muke ciki bane?

Wane shiri PDP ta yi?

Ortom ya ƙara da cewa sakamakon da kowa ya gani na babban taron PDP na ƙasa babbar alama ce ta cewa jam'iyyar ta shirya kwace mulki a 2023.

"Mu a PDP babu makawa zamu karbi mulki a 2023, saboda gazawar gwamnatin APC. Sun yaudari mutane kuma sun kasa ceto ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Gwamnan APC ya bayyana rawar da ya taka wajen tsige kakakin majalisar dokokin Filato

"Maimakon haka sai suka cigaba da rusa mana tattalin arziki, tsaro, walwala da jin dadi da sauran duk abinda zaka iya lissafowa a ƙasar nan."

A wani labarin kuma Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokokin Filato ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

A halin yanzun wasu matasa da ake tsammanin magoya bayan sabon kakakin majalisa ne, Yakubu Sanda, sun kutsa kai cikin zauren ta kofar baya.

Hakan ya harzuƙa magoya bayan tsohon kakaki, amma jami'an tsaro suka fara harbi a iska domin kwantar da tarzomar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel