Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara

Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara

  • Gwamna Ganduje ya koka kan yadda iyaye ke tilastawa'ya'yansu barace-barace a Arewacin Najeriya
  • Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin mummunan abu, Kuma hakan cin zarafin yara ne kanana
  • Gwamnan a kasafin kudin 2022, ya ware makudan kudade don tallafawa harkar ilimi a jihar Kano

Kano - Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan mugun halin wasu iyaye a yankin arewacin kasar nan da ke tilastawa 'ya'yan su barace-barace yana mai bayyana hakan a matsayin cin zarafi.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa lokaci ya yi da dokokin tarayya za su kara kaimi wajen kafa dokar hana barace-barace a duk sassan kasar nan, jaridar Leadership ta ruwaito.

Wasu iyaye na cin zarafin 'ya'yansu: Ganduje ya koka kan iyaye masu tura 'ya'yansu bara
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Depositphotos

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin taron kasa karo na biyu da tsangayar ilimi ta Jami’ar Bayero da ke Kano ta shirya, ya bayyana cewa dokar za ta tilastawa iyaye/iyayen riko su saka ‘ya’yansu a makaranta.

Kara karanta wannan

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

Ya kara da cewa kalubalen tsaro da ayyukan ta’addanci sun haifar da karin matsaloli a bangaren ilimi a yankin Arewa maso Gabas da wasu jihohin Arewa maso yammacin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban taron Farfesa Abdulrasheed Garba ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta ware sama da 26% na kasafin kudinta na 2022 ga fannin ilimi, sannan ya bukaci sauran gwamnatocin jihohi su yi koyi da hakan.

Gwamna Ganduje ya jima yana fada da yawaitar barace-barace a Arewacin Najeriya, musamman jiharsa ta Kano.

A shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito yadda gwamnan ya Hana barace-barace a jihar Kano ba ga yara kadai ba, har ma ga masu manyan shekaru.

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

A wani labarin, Kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar shirye-shiryenta na tallafi ta farfado da rayuwar miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin Borno da Arewa maso Gabas, in ji shugabar tawagarta a Najeriya da ECOWAS, Ambasada Samuela Isopi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata

Ta ce kungiyar ta EU ta bada kudi kusan Yuro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da suka gabata don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Borno na sake ginawa da kuma gyara al’ummomin da abin ya shafa, Leadership ta ruwaito.

Wannan tallafin kudade kadai, a cewarta, ya taimaka wajen maido da ababen more rayuwa a fannoni da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel