Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

  • Ido dai ya karkata ga jam'iyyar PDP yayin da jam'iyyar ke zabar sabbin jami'anta na kasa a taron gangaminta na kasa
  • ‘Yan jam’iyyar na fatan taron zai zama wani sabon yanayi ga jam’iyyar PDP bayan da ta shafe tsawon lokaci na danbarwa a shugabancinta
  • Wani fitaccen jigon jam’iyyar, Osita Chidoka, ya zayyana batutuwan da ya kamata PDP ta mayar da hankali wajen ci gaba

Abuja - Cif Osita Chidoka, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya bayyana ra’ayinsa kan abin da ya kamata sabbin shugabannin jam’iyyar PDP su yi bayan taron gangamin jam’iyyar da ke gudana a dandalin Eagles Square da ke Abuja.

Taron dai ya shaida fitowar sabbin mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP.

Da yake rubuta ra'ayinsa a shafinsa na Facebook, Chidoka ya bayyana kwarin gwiwar cewa taron zai yi kyau, kuma za a zabi sabbin mambobin NWC ba tare da wata tangarda ba.

Kara karanta wannan

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

Jigon PDP ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya
Cif Osita Chidoka | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya rubuta cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin da ya dameni shine washegarin taron; menene ajanda ga sabbin membobin NWC?”

Ya jera shawarwarinsa da suka hada da:

1. Tabbatar da jam'iyyar a matsayin jam'iyya ta kasa ta gaske mai bin tsarin laima

2. Samar da tsare-tsare da suka dace da kuma manufofin ceto Najeriya

3. Kauce ficewar manyan jiga-jigan jam'iyyar da sake gina jam'iyyar a shiyyar arewa maso yamma da arewa maso gabas.

4. Damawa da sabbin jinin masu jefa kuri'a da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 wadanda ba za su iya tuna shekarun mulkin PDP na 2003 zuwa 2014

5. Gina tsarin jam'iyya na zamani da na zabe daidai da INEC da kuma iya fitar da dan takarar PDP a 2023.

6. Kirkirar sabon labari wanda na bai daya, da bege, da sa ido. Wa'adin Shugaba Buhari ya kare, Najeriya ta durkushe ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Sanata Kwankwaso ya yi magana a kan sake sauya-sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC

Shin PDP za ta iya sake mayar da hankali kan sakon ta don ba da hanyoyin da za su dace da kuma inganta tushenta yayin da ba a yanke shawara ba?

7. Bayan taron gangamin, muna bukatar taron siyasa. Muna bukatar sake daidaituwa. PDP ba ta cin gajiyar mulkin APC, wannan batu na gaskiya dole ya sauya

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

A bangare guda, Shugaban kwamitin karramawa na taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ifeanyi Okowa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, ya ce tsare-tsare da sakamakon atisayen zai tabbatar da cewa jam’iyyar a shirye take ta ceto Najeriya daga kalubalen da ke addabarta.

Okowa, wanda shine gwamnan jihar Delta ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron kwamitin da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja.

Ya ce jam’iyyar PDP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa taron zai karfafa hadin kai da dimokradiyya ba a jam’iyyar kadai ba har ma a kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel