Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

  • Komai ya gudana a taron gangamin jam’iyyar PDP a Abuja kuma Gwamna Ifeanyi Okowa na da kwarin gwiwar cewa wannan atisayen zai sauya fasalin siyasar Najeriya
  • A cewar gwamnan na jihar Delta, taron zai nuna wa jam’iyyar APC mai mulki cewa lokacinta ya zo karshe a matakin tarayya
  • Ranar Asabar aka fara gudunar da taron gangamin, taron da ya sami halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar ta PDP

Shugaban kwamitin karramawa na taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ifeanyi Okowa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, ya ce tsare-tsare da sakamakon atisayen zai tabbatar da cewa jam’iyyar a shirye take ta ceto Najeriya daga kalubalen da ke addabarta.

Okowa, wanda shine gwamnan jihar Delta ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron kwamitin da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

Daga taron gangamin PDP, karshe APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani Gwamna
Wurin taron gangamin PDP | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce jam’iyyar PDP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa taron zai karfafa hadin kai da dimokradiyya ba a jam’iyyar kadai ba har ma a kasar baki daya.

An zabi shugabannin PDP

A rahotanni da Legit.ng ke samu, tuni taron gangamin ya kai ga zaben shugabannin PDP, inda aka bayyan sunayen wasu 21 da suka yi nasarar lashe kujerun shugabancin jam'iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels ta ruwaito cewa, an zabi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, kuma har ya fito a filin taron ya yi jawabin godiya ga ilahirin 'yan jam'iyya.

Shi ma a bangarensa, Ayu ya shaida cewa, PDP ta shirya tsaf don kubutar da Najeriya daga halin da ta ke ciki.

Fastocin neman tsayawa takarar kujerun siyasa daban-daban sun bayyana a taron gangamin PDP

Kara karanta wannan

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

A baya kun ji cewa, dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da taron gangamin jam’iyyar adawa ta PDP, a halin yanzu yana cike da tutoci da fastocin talla daban-daban na ‘yan takarar siyasa.

Wasu daga cikin fastocin sun hada da na gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Hakazalika da tsohon dan sanata, Shehu Sani; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas; Doyin Okupe; Gwamna Aminu Tambuwal da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel