Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

  • Wata kungiyar mata ta bayyana yiyuwar maka jam'iyyar PDP a kotu bisa zargin nuna wariyar fata ga mata 'yan siyasa
  • Kungiyar ta koka kan yadda jam'iyyun siyasa ke kebe mata a gefe idan ana batun ba da mukamai a jam'iyyun
  • Hakazalika, kungiyar ta nemi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dauki mataki kan irin wannan batu

Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Wata kungiyar mata ‘yan siyasa ta Women in Politics Forum (WIPF), a jiya Laraba ta yi barazanar kai karar jam’iyyar PDP, kan wani shiri na mayar da mata bare a taron gangaminta na kasa da ke tafe.

Kungiyar ta yi zargin cewa jam’iyyar na kokarin kefe mata a yayin taron gangamin da aka shirya gudanarwa a tsakanin ranakun 30 zuwa 31 ga watan Oktoba, 2021 ta hanyar samar da wani tsari na bai daya da ya karkata wajen ganin maza su raba mukaman jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Rikicin PDP: Ba a gama da rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu
Matan jam'iyyar PDP | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan, a cewarsu, ya saba kaso 35 na tabbatar da matakin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Shugabar WIPF, Ebere Ifendu ne ta yi wannan barazanar a wani taron manema labarai a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce abin takaici ne a ce duk da tanade-tanaden da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada, mazan da suka mamaye shugabancin jam’iyyar sun ci gaba da amincewa da ba maza mukamai daban-daban a karkashin yarjejeniya.

Ta bayyana goyon bayan kungiyar ga burin tsohuwar ministar harkokin mata, Inna Ciroma, wacce ke neman mukamin mataimakiyar shugabar jam'iyya ta kasa (Arewa).

Ifendu ta ce a matsayin nuna goyon baya, mambobin WIPF sun biya kuma sun samu fom din takarar mataimakiyar jam'iyyar.

Ta kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta samar da wani tanadi da zai kare hakkin mata yayin da take gabatar da gyara ga dokokin zabe.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

Ta koka kan yadda jam'iyyun siyasa ke keta dokokin jam'iyyar, a bangare guda kuma INEC ba ta daukar wani mataki.

A ba mata rikon Najeriya

Da ake batun shugabancin mata, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, yace mata suna da kwarewar da zasu ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta idan aka basu dama.

The Nation ta ruwaito cewa Gwamnan na ganin tun da maza sun gaza gyara Najeriya, wannan lokacin ne da ya dace mata su shugabanci kasar nan.

Gwamna Akeredolu ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabin buɗe babban taron mata (NWC), karo na 21, wanda ƙungiyar matan Legas (COWLSO) ta shirya.

2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna

A wani labarin, Gwamnan jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel ya ce akwai fatan alheri ga ‘yan Najeriya idan aka yi la’akari da gagarumin nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a matsayin jam’iyya a kasar.

Kara karanta wannan

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a Uyo, yayin da yake kaddamar da rajistar ranar gizo na mambobin jam’iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom.

Ya yi nuni da cewa irin kukan da ‘yan Nijeriya ke yi a halin yanzu saboda rashin shugabanci nagari, za a iya magance shi ta hanyar shugabanni masu kishin jama’a da jam’iyya irin ta PDP ke da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel