Sanata Kwankwaso ya yi magana a kan sake sauya-sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC

Sanata Kwankwaso ya yi magana a kan sake sauya-sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya karyata rade-radin cewa akwai yiwuwar ya koma jam’iyyar APC mai mulki
  • Tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya bayyana cewa har gobe yana nan jam’iyyar hamayya ta PDP
  • Da aka yi hira da Kwankwaso a gidan talabijin dazu, yace zai cigaba da bada gudumuwa a jam’iyya

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a game da rade-radin da ake yi na cewa yana shirin barin PDP.

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana nan a jam’iyyar PDP. Kwankwaso ya yi karin-haske da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise.

Shugaban darikar siyasar Kwankwasiyyan ya yi wannan martani ne yayin da aka jefa masa tambaya kai-tsaye da ake hira da shi a game da makomarsa.

Kara karanta wannan

Ina gwamna ban taba karbo bashin ko kwandala daya ba, Kwankwaso ya sake caccakar Ganduje

“Har yanzu ni ‘dan jam’iyyar PDP ne.” - Kwankwaso

Tsohon Ministan yace zai yi zamansa a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya hada-kai da sauran abokan aikinsa wajen ganin an shawo kan rikicin cikin gidansu.

Sanata Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

A kwanakin baya ‘dan siyasar ya tabbatar da cewa ya fara jan-kafa daga al’amuran PDP a dalilin sabanin da ya samu da wani gwamna a Arewacin Najeriya.

Yayin da jam’iyyar PDP ke cikin rikicin gida, Kwankwaso yace zai ta bada gudumuwar kawo mafita.

Rikicin cikin gidan jam’iyyar PDP

A hirar da ‘yan jarida suka yi da Kwankwaso a yau Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, ya yi magana a kan rigimar da ake fama da ita a jam’iyyar PDP.

Rabiu Kwankwaso yace da an ji shawara, da ba za ayi da fama da rigingimu a jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna

Sanata Kwankwaso wanda ya wakilci Kano a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 yace Uche Secondus ya jawo rashin tabbas a dalilin karar da ya kai kotu.

A lokacin da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suke tunanin zuwa birnin tarayya Abuja domin zaben shugabanni na kasa, kan wasu ya rabu a kan yiwuwar zaben.

Sabani tsakanin 'ya 'yan APC

Yunkurin yin sulhu a Jam’iyyar APC mai mulki ya fara cin tura a Kano, Ogun da wasu Jihohin da ake rigima tsakanin kusoshin jam'iyya da kuma gwamnoninsu.

Wadanda suka ware sun yi zaben su dabam a kwanaki. APC na fama da wannan rikici tsakanin tsagin Ibrahim Shekarau da Gwamna Abdullahi Ganduje a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel