Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

  • Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, bai halarci filin taron jam'iyyarsa ta PDP ba ranar Asabar
  • Rahoto ya bayyana cewa Jonathan ya faɗa wa gwamnonin PDP biyu da suka ziyarce shi cewa ba zai halarta ba saboda zai bar Najeriya
  • Gwaamnonin sun roki babban jigon na PDP da ya halarci wurin kuma ya bada jawabinsa kafin ya kama hanyar fita kasar

Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda babban jigo ne a PDP, bai sami halartar babban gangamin taron PDP na ƙasa ba ranar Asabar.

Premium Times ta rahoto cewa Jonathan ya bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron ƙungiyar Nahiyar Africa a Nairobi, Kenya, wanda za'a tattauna kan zaman lafiya a Africa.

Amma wasu ƙusoshin PDP na ganin tsohon shugaban ya yi amfani da wannan uzurin ne domin tsallake babban gangamin PDP.

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali zan nemi kujerar shugaban ƙasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

Goodluck Jonathan
Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP Hoto: @Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Yadda wasu jigogin PDP ke kallon lamarin

Wani ƙusa a jam'iyyar PDP yace:

"Idan har hankalinsa nakan taron, da kuma harkokin jam'iyya da ya halarci wurin na ɗan lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi ranar Asabar.
"Hakanan kuma zai iya turo tsohon mataimakinsa, Namadi Sambo, ko wani na kusa da shi, domin ya yi fatan alkairi a taron a madadinsa."

Wata majiya daga cikin PDP, ta bayyana cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gana da Jonathan ranar Jumu'a.

Me suka tattaunaa da shi?

Majiyar ya ƙara da cewa lokacin da Jonathan ya faɗa musu zai tafi Nairobi, gwamnonin biyu sun bukaci ya halarci wurin taron na ƙanƙanin lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi.

Hakanan gwamnonin sun masa tayin cewa zasu shirya masa tafiyar da zai yi bayan an kammala taron, amma tsohon shugaban ya ƙi amincewa.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

Yayin da aka tuntubi kakakin Jonathan, Ikechukwu Eze, ranar Lahadi da safe, ya bukaci a tura masa takar da ta shafinsa na WhatsApp.

Sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto Mista Eze bai maido da amsa ba kan haƙiƙanin ganawar gwamnonin da uban gidansa.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Lalong na jihar Filato yace yasan radadin tsige mutum daga mukamin shugaban majalisa

Gwamnan ya kuma musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa shine ya haɗa komai ya bada umarnin cire kakakin majalisar dokokin Filato.

Gwamnan yace ɓangaren majlisa zaman kansa yake, kuma suna tafiyar da harkokinsu ba tare da jiran umarnin wani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel