Taron Gangamin PDP: Fastoci sun bayyana, Bala da takarar shugaban kasa, Shehu Sani kuma gwamna

Taron Gangamin PDP: Fastoci sun bayyana, Bala da takarar shugaban kasa, Shehu Sani kuma gwamna

  • Da farko dai ana gudanar da taron gangamin jam'iyyar PDP na kasa ne domin zaben sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na kasa (NWC)
  • Sai dai kuma al’amuran da ke faruwa na nuni da cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP na iya fara amfani wannan gagarumin taron domin bayyana burinsu na tsayawa takara kafin 2023
  • Hotunan da ke nuna Bala Mohammed a matsayin dan takarar shugaban kasa, Shehu Sani; gwamnan Kaduna, da dai sauransu, sun mamaye dandalin Eagles Square, wurin taron

Abuja - Dandalin Eagle Square, wurin da ake gudanar da taron gangamin jam’iyyar adawa ta PDP, a halin yanzu yana cike da tutoci da fastocin talla daban-daban na ‘yan takarar siyasa.

Wasu daga cikin fastocin sun hada da na gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa

Hakazalika da tsohon dan sanata, Shehu Sani; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas; Doyin Okupe; Gwamna Aminu Tambuwal da sauran su.

Taron Gangamin PDP: Fastoci sun bayyana, Bala takarar shugaban kasa, Shehu Sani gwamna
Wasu daga cikin jiga-jigan PDP | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Legit.ng gano cewa, yayin da fastocin Sanata Bala Mohammed, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suka bayyana neman shugabancin kasa, Shehu Sani kuwa yana neman gwamna a Kaduna 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fastocin da suka fi girma kuma suka fi bazuwa su ne na Sanata Bala Mohammed wanda manyan tutoci suka bazu ko'ina a fadin wurin taron ciki har da yankin manyan baki.

Haka kuma a kewaye da wurin taron, akwai tutoci da ke nuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

An kuma gano tutocin Okupe a ciki da wajen filin taron.

Yayin da wasu daga cikin fastocinsa ba su nuna wani matsayi da kakakin tsohon shugaban kasar zai yi nema ba, wata fosta ta musamman tana dauke da "Okupe for President 2023".

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Shugaban APC Buni da tawagarsa sun ziyarci Tinubu a gidansa

Taron gangamin na jam’iyyar PDP na kasa ya samu izini daga kotun daukaka kara bayan takaddamar shari’a da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus.

Secondus dai ya shigar da kara ne a gaban kotu domin hana jam’iyyar PDP ci gaba da shirin gudanar da taron gangamin.

A karar da ya shigar, Secondus ya ce ya kamata kotu ta bayar da umarnin dakatar da taron jam’iyyar PDP na kasa har sai an yanke hukunci na karshe kan lamarin da ke gabanta.

Sai dai kuma a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Secondus a kan taron gangamin jam’iyyar da aka shirya yi saboda rashin cancanta.

Tuni dai shugaban jam’iyyar PDP na kasa da aka dakatar ya mayar da martani ga hukuncin kotun inda ya bayyana cewa zai nemi a yi masa hukunci a kotun koli.

Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma

Kara karanta wannan

Jiga-Jigai da mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar

Jiga-jigan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a jihar Ondo sun yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.

An cimma matsayarsu ta komawa jam'iyyar PDP ne a wani taro da aka yi a garin Ondo da shugaban jam'iyyar ZLP na kasa Dr. Olusegun Mimiko. Wannan dai shi ne karo na uku da Mimiko zai sauya sheka zuwa PDP.

Sauran shugabannin ZLP da suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin gwamnan Ondo Agboola Ajayi; Hon Gboye Adegbenro da tsohuwar kakakin majalisar Ondo Jumoke Akindele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel